An Kashe Kwamandan Rundunar Community Watch a Karamar hukumar Safana
- Katsina City News
- 13 Nov, 2023
- 1327
AN KASHE KWAMANDAN " COMMUNITY WATCH" A SAFANA.
Daga Muhammad Bello @ Katsina Times.
Yan ta adda sun kashe wani kwamandan sabuwar rundunar nan ta Katsina Community Watch mai kula da garin Zakka ta karamar hukumar Safana.
Kwamandan Wanda yake kula da yankin Zakka mai suna Mujitaba Salisu an kashe shi ne tare da wani Dan sandan Mobayil (Mobile Police).
Wani a garin Zakka ya fada ma jaridun Katsina Times cewar, a jiya lahadi 12 ga watan Nawumba, 'Yan ta addar suka fito daga daji suka tunkaro Zakka.
Ganin sun nufo garin yan sanda da Hadin gwaiwar yan Katsina Community Watch dake garin na zakka suka fuskance su inda akayi fadan gaba da gaba.
A wannan bata kashin ne aka kashe Mujtaba da Dan sanda daya, suma barayin anyi masu Barna sosai amma sun tafi da gawarwakin mutanen su.
Wata majiya tace, Barayin Sun yi yunkurin yin gangami domin karasa ta addacin da suka shirya, amma sai sojan sama suka kawo dauki Wanda wannan ya tsorata barayin suka koma daji.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
07043777779 08057777762.