"Gwamnatin Tarayya ba zata cigaba da zura ido akan gidajen da ake fara ginawa a watsar dasu ba" Dangiwa
- Katsina City News
- 10 Nov, 2023
- 695
A Wani kakkausan Gargadi Ga Ƴan kwangila, Ministan Gidaje da Raya Birane Ahmed Dangiwa ya bayyana Cewa Gwamnatin Tarayya baza ta Cigaba da lamuntar ayyukan Gidaje da akayi watsi dasu a faɗin ƙasar ba.
A yayin ziyarar sanin makamar aiki da aka bayar a Shekarar 2019, Dangiwa ya duba rukunin Gidaje 1,250 Brains and Hammers Estate da ke Jibi, Abuja, da kuma wani rukunin Gidaje Guda 24, wanda ya kunshi Gidaje 1, 2, da 3.
Ya nuna rashin jin dadinsa da ganin wuraren gine-gine da aka yi watsi da su, inda ya yi kira ga masu aikin gina gine-gine da su kawar da duk wani ciyayi da tarkace daga wuraren cikin Gaggawa.
“Ba za mu kara lamuntar duk wasu ayyukan da aka yi watsi da su ba,” in ji Dangiwa. "Muna da niyyar mayar da hannun jarin da Gwamnati ta yi tun da farko. Don haka duk wuraren gine-gine da aka yi watsi da su, muna Gayyatar duk masu aikin ginawa da su zo su zauna tare da mu su san dalilin da ya sa suka yi watsi da shi."
Dangiwa ya jaddada cewa abin da gwamnati ta sa gaba shi ne samar wa ‘yan Najeriya gidaje masu saukin kudi, inda ya ce shugaba Bola Tinubu na da kishin wannan al’amari.