AN KAI MUMMUNAN HARI KARAMAR HUKUMAR FASKARI JAHAR KATSINA
- Katsina City News
- 10 Nov, 2023
- 1103
Muhammad Yankara @Katsina Times
A Jiya Alhamis 9/11/2023 Wasu Yan ta adda masu Garkuwa da Mutane suka kai Hari garin zagami dake yankin yankara karamar hukumar faskari.
Maharan Sun kashe Mutum daya da kwasar Mutanen dayawa Wadan da har yanzu Ba a tantance Adadin su ba.
Maharan sun auka a taron Muhalin Maulid Annabi Muhammad (S.A.W.W.) a garin Zagami da ke 'Yankin 'Yankara a karamar Hukumar Faskari Jihar Katsina.
A wajen Misalin Karfe 12:00 na Dare
Wani da akayi abin gaban sa mai suna Ibrahim Alale Adamu zagami ya shaida ma Katsina Times Cewar, taron yana tsakiyar tafiya lami lafiya, sai kawai sukaji Hari ko ta na ina.
Adamu Alale, yace daga cikin wadanda maharan suka tafi dasu cikin daji harda wani Babban Malami da yazo daga kasar Ghana.
Adamu Alale yace ba a iya tantance yawan wadanda suka tafi dasu daji saboda fashewa akayi aka tarwatse kowa na ta ransa.
Munyi kokarin jin ta bakin rundunar yan sanda ta jahar Katsina amma ba muyi nasara ba.don wayar kakakin yan sanda bata shiga.
Wannan sabon salo na kai Hari ga masu taron addini ana ganin shi a wani sabon salo Wanda yan ta addar daji suka shigo daji.wanda ake gani bai rasa nasaba da yan kungiyar Iswap da suka fara aiki tare da barayin na daji.su kuma yan iswap sun dauka taron Maulud kafirci ne.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
07043777779 08057777762