'Yan Bindiga sunkai mummunan hari a garin Sayaya ƙaramar hukumar Matazu jihar Katsina
- Katsina City News
- 07 Nov, 2023
- 717
Ƴan ta'addar daji ɗauke da muggan makamai sun kai harin Ta'addanci a ƙauyen Sayaya dake ƙaramar hukumar Matazu jihar Katsina, wani da harin ya rutsa da mahaifin shi ya bayyana cewa ƴan ta'addar sun shiga gida-gida a garin na Sayaya a ƙaramar hukumar Matazu suka kashe kimanin Mutane Biyar 5 ciki har da mahaifin nashi - Inji Ahmad Ibrahim
Cikin daren jiya Litinin wayewar garin yau Talata ƴan bindigar suka shiga cikin garin na Sayaya, kuma sun kore shanayen mutane masu yawa, kimanin Mutane Biyu kuma sun samu raunika yayinda ɓarayin suka sace kimanin Mutane Biyar suka tafi dasu daji.
Rundunar Ƴansandan jihar Katsina ta bakin mai Magana da yawun ta ASP Abubakar Sadiq Aliyu ta tabbatar da faruwar Lamarin.
Wannan dai na zuwa ne bayan a daran ranar Litinin kuma wasu ƴan bindigar suka buɗe wa masu bikin mauludi wuta, a yankin ƙaramar hukumar Musawa dake makwabtaka da Matazun, inda ko a nan ma sai da ƴan bindigar suka kashe mutum 13, tare da jikkata kusan mutum 20 da munanan raunuka na harbin bindiga, kazalika anan ma sun ƙwashe wasu Mutanen zuwa daji.