Fadi-tashin-yaki da ’yan ta’adda: Irin tsarin Dikko Radda (Gwagware)
- Katsina City News
- 02 Nov, 2023
- 666
Daga Mannir Shehu Wurma PhD.
Fiye da makonni hudu, na yi ta yunkurin fadin ra’ayi ne game da ayyukan Gwamnatin Jihar Katsina da kuma matakan tsaron da take dauka musamman. Sai dai a dukkanin tsawon wannan lokacin, ina fama da rashin sanin wadanne kalmomin ne zan yi amfani da su da za su dace da wannan yanayin ko tsarin da ake da shi a kasa.
Gwamna Malam Dikko Radda ya cancanci samun wannan sarauta ta Gwagware da ke girman matsayi a Masarautar Katsina.
Malam Dikko Umar Radda shi ne Gwamnan Jihar Katsina kuma mai rike da sarautar Gwagwaren Katsina. Gwagwaren Katsina wani mashahurin mayaki ne a masarautar Katsina a Karni na 17. Labarin Gwagwaren Katsina na farko a tarihi shi ne wanda ya yaki rashin gaskiya da adalci, tawaye da kuma sata da garkuwa da mutane.
An kuma nada Gwamna Radda Gwagware Katsina shekaru 15 da suka gabata, wanda hakan ke nufin mayaki ne a Katsina tuntuntuni kafin ya zama gwamnan Katsina.
Ko kana sane da ma’anar Gwagware ko matsayinta ta a tsarin sarautar Katsina? Domin ba da amsar wannan irin kokari da yunkuri da tsayin daka da sadaukarwar Malam Dikko Radda. Ya yi imanin cewa da yardar Mai Duka, Allah zai kawo karshen masu garkuwa da mutane da barayin shanu da sauran matsalolin da ake fama da su a Jihar Katsina.
Mahimmancin Kwamitin Tsaro na Jihar Katsina ya wuce a kwatanta shi. A karon farko, muna da Gwamna wanda ya fahimci irin wahalhalun da jama’a ke fama da shi, kuma ya amince ya yaki wannan matsala lokaci guda kowa ya huta.
Saboda haka kaddamar wannan tsarin tsaron ya ba kowa mamaki, kuma ya rufe bakunan kowa. Na yi imanin cewa su kansu ’yan fashin dajin, tsoro da tashin hankali ya shiga ransu da ganin wannan. Idan da kana nan ko ka ga hotuna da ka samu kwanciyar hankali, domin sanin cewa wannan karon ’yan fashin daji za su gwammacewa kida da karatu. Yanzu ne lokacin daukar mataki.
Kafin Gwagware ya gabatar da shirinsa na tsaro, jama’a sun yanke kauna, sun mika wuya da kuma yunkurin tabukawa wajen kare kansu.
Daga yadda aka tsara ayyukan wannan kwamitin tsaron, mun amince cewa lallai wannan karon gwamnati da gaske take na yunkurin ganin bayan rashin tsaro da ke damun al’ummarmu. Babu kokwanto, wannan matsalar mai sarkakiya, wajibi ce dukkaninmu mu ba da gudummuwarmu ta hanyar samar da dukkanin wasu bayanai na tsaro da za su taimaka wajen nasarar wannan shirin.
MANNIR SHEHU WURMA, lakchara ne. kuma yanzu shi ne Shugaban karamar Hukumar Kurfi.jahar Katsina