ANYI MA WANI YARO YANKAN RAGO A BATSARI
- Katsina City News
- 31 Oct, 2023
- 619
Misbahu Ahmad Batsari
@ Katsina Times
Da misalin ƙarfe tara na daren ranar litanin 30-10-2023, aka hallaka wani yaro ta hanyar yanka da wuƙa a Unguwar mata mulki dake cikin garin Batsari hedikwatar ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Shedun gani da ido sun bayyana mana cewa, wani matashi mai suna Nasiru Sangami ɗan kimanin shekaru talatin ya lallaɓi wani yaro mai suna Ali ɗan shekara takwas, inda yaje da shi wani kango yasa wuƙa ya gagure masa wuya ya mutu har lahira.
Makusantan yaron sunyi ta faman neman yaron, amma basu gane inda ya tafi ba, sai daga bisani aka tsinci gawar sa cikin wani kango.
Da aka tsananta bincike sai aka gano cewa Sangami ne ya tafi da shi ya hallaka shi wanda jami'an community watch suka cafke shi kuma take ya amsa laifin sa, daga nan kuma suka miƙa shi ga jami'an ƴan sanda domin cigaba da bincike da ɗaukar matakin da ya dace.
Wakilinmu ya tuntubi jami an yan sanda na karamar hukumar Batsari suka ce yayi magana da hedkwatar yan sanda ta jaha.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779.08057777762