MAJALIASAR DOKOKIN KATSINA TA KAFA KWAMITIN BINCIKEN RUBUTUN DA AKA ZARGE TA AKAN MAKARANTAR KSITM.
- Katsina City News
- 18 Oct, 2023
- 882
Muazu Hassan. Katsina Times
Majalisar dokokin jahar Katsina ta kafa wani Kwamiti da zai binciki wani rubutun da wasu da a ake zargi kuma yan sanda ke bincike suka yi.karkashin wata kungiyar da babu ita, bata da rijista mai suna Katsina watch.
A cikin rubutun wadanda an rubuta cewa, shugaban makarantar KSITM Dakta Babangida Albaba yayi amfani da dan uwansa Dan majalisar dokokin jahar Katsina domin yin ba dai dai ba a canza sunan makarantar.
Majalisar ta dokokin a zaman ta na ranar talata 17 ga watan oktoba ta kafa Kwamiti kuma ta bashi sati biyu daya binciki wancan zargin da aka rubuta ya kuma kawo ma ta rahoto cikin cikakke cikin sati biyu.
Majalisar tace,duk abun da binciken su ya gano zasu bi hakki da kuma Daukar matakin shara a ga duk Wanda yayi ma majalisar kazafi ko kuma Danta.
Majalisar tace, abin dake cikin rubutun karya ce muraran.babu ita,ba kuma wata bukata a gaban majalisar mai sunan wannan.suka ce amma a bincika
A kwanakin baya ne, wasu da ba asan ko su waye ba suka rika rubuce rubucen zarge zarge akan shugaban makarantar KISM Katsina dakta Babangida Albaba.
Dakta Babangida Albaba ya kai kara wajen yan sanda domin yana neman a binciko su waye kuma a bi masa hakkin shi.
A binciken yan sanda sun gayyaci rijistara na makarantar da kuma mataimakin Basa.wadanda suka zama Manyan wadanda yan sanda ke zargi.
Yan sanda sun kuma Kira mutane da yawa wadanda suka taimaka masu da bayanan da suka taimaka ma binciken nasu.
Majiya a hukumar yan sanda sun tabbatar da jaridun,mu da cewa sun kammala binciken su.kuma Suna da hujjojin da zasu iya kai mutane biyu gaban kotu.
Ana tsakar haka sai gwamnatin Katsina ta kafa Kwamitin da zai Duba ayyukan makarantar tun daga kafata zuwa yanzu..ciki har da duk wani zarge zarge da ya shafi makarantar.
Kwamitin ya hada mutane masu mutunci da aka sansu da dattaku da kuma tsare gaskiya a aiki.karkashin jagoranci Alhaji AD Umar tsohon babban sakatare a gwamnatin jahar Katsina.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
All in All social media platforms
07043777779 08057777762