Tarihin Unguwar Malumma a cikin Birnin Katsina
- Katsina City News
- 16 Oct, 2023
- 894
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Malumma tana nan yamma da tsohuwar Kasuwar Katsina. Daga kudu tayi iyaka da Gambarawa. Ta bangaren Arewa tayi iyaka da Farin Yaro, ta bangaren yamma ta yi iyaka da kofar guga, sannan ta bangaren gabas tayi iyaka da gidauniyar Ilimi ta jihar Katsina.
Kamar yanda sunan ya nuna, Malumma unguwa ce ta Malamai.
Tarihi ya nuna cewa Malam Usman da Malam Joɗoma wanda aka fi sani da suna Wali Joɗoma, su ne suka kafa Unguwar. Asalin Mutanen Barno ne, Malam Usman yazo Katsina ne tare da Matarsa wadda ake kira da suna Maimunatu. Shi kuma Abokinsa da ake kira Malam Joɗoma ance bai taɓa haihuwa ba.
Lokacin da malam Usman da Malam Joɗoma suka isa birnin katsina sai sarkin Katsina ya turasu wajen mai Unguwar Gambarawa domin ya samar masu wajen zama. Mai unguwa ya basu waje suka kafa Bukkokinsu. Daga nana sai suka cigaba da harkokinsu na karantar da ilimin Addinin Musulunci. Daga nan sai mutane suka dunga kiran wajen da sunan Malumma.
Baya ga harkar Malumta, mutanen Malumma suna gudanar sauran sana'o,i kamar Noma, Sayar da Turare Halawa, Ƙuli-ƙuli da sauransu. Wadannan sana'o,i sun bunkasa ƙwarai da gaske a Unguwar Malumma kasancewar ta kusa da tsohuwar Kasuwar Katsina.
Tarihi ya nuna cewa a unguwar Malumma ne aka fara sarautar Sarkin Turare a Katsina. Wanda ya fara wannan sarautar shine Marigayi Alhaji Sabi'u mai Turare. Sarkin Katsina Alhaji Usman Nagogo ne ya naɗa shi wannan sarauta.
Daga cikin abubuwan Tarihin da aka yi a unguwar Malumma akwai "Cediyar Bakwai" da "Tafkin Dungure" da "Tafkin Suda". Akwai kuma Malamai masana kamar Malam Mani Bazanfare da Malam Manzo da sauransu. Cikin jikokin Wali Joɗoma akwai Marigayi Alhaji Sabi'u da Alhaji Ali Babangida da Malam Amiru da kuma Malam Rabi'u.
Mun ciro wannan "Tarihi daga Littafin Tarihin Unguwannin Birnin Katsina" na Hukumar Binciken Tarihi da kyautata Al'adu Ta jihar Katsina