Ma’aikatan Karamar Hukumar Musawa Sun Koka Kan Nada Ma’aji

Daga Hadi Abdullahi@ Katsina TimesWasu ma’aikatan Karamar Hukumar Musawa a Jihar Katsina sun bayyana takaici da korafinsu kan yadda aka ce an tura wani ma’aikaci da ba shi da ilimin…

Katsina City News September 02, 2026  ·  12:00 AM
| 129 Views
Ma’aikatan Karamar Hukumar Musawa Sun Koka Kan Nada Ma’aji
Ma’aikatan Karamar Hukumar Musawa Sun Koka Kan Nada Ma’aji


Daga Hadi Abdullahi

@ Katsina Times

Wasu ma’aikatan Karamar Hukumar Musawa a Jihar Katsina sun bayyana takaici da korafinsu kan yadda aka ce an tura wani ma’aikaci da ba shi da ilimin harkokin kuɗi domin ya zama Ma’aji na karamar hukumar.

Wani jigo a ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi daga Musawa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya jagoranci wasu daga cikin ma’aikatan zuwa ofishin Katsina Times, inda suka bayyana korafinsu tare da roƙon Gwamnan Jihar Katsina da ya binciki lamarin.

Ma’aikatan sun ce mutumin da aka naɗa, mai suna Bello Usman, yana da digiri a fannin Ilimin Mulki, wanda suka ce ba fannin harkokin kuɗi ba ne.

Sun ce sun gabatar wa da jaridar Katsina Times wasu hujjoji da suka shafi takardun karatu da ƙwarewar wanda aka naɗa.

A cewarsu, akwai ƙwararrun ma’aikata a Sashen Kuɗi na Karamar Hukumar Musawa waɗanda suke da digiri da sauran ƙwarewa a fannin harkokin kuɗi, tare da gogewar aiki.

“Idan za a gudanar da jarabawa kan wannan fanni, akwai ma’aikatan da suka ƙware sosai kuma suka dace da wannan matsayi,” in ji ɗaya daga cikin ma’aikatan.

Sai dai sun yi zargin cewa an tsallake irin waɗannan ma’aikata, aka naɗa wani da suka ce ya fito daga wani fanni daban domin ya zama Ma’aji na karamar hukumar.

Ma’aikatan sun kuma yi zargin cewa sabon wanda aka ba matsayin yana fuskantar ƙalubale wajen gudanar da wasu ayyukan da suka shafi mukaminsa, inda suka ce wasu ayyukan sun tsaya saboda yana ƙoƙarin fahimtar yadda ake gudanar da aikin.

A cewarsu, wannan mataki ya saɓa da tsarin cancanta da ƙwarewa da suke ganin gwamnatin Gwamnan Jihar Katsina ke ƙoƙarin tabbatarwa.

Sun roƙi Gwamnan Jihar Katsina da ya sa a binciki lamarin tare da ɗaukar matakin da ya dace.

Advertisement

NRS Gateway

“Ya kamata a bai wa waɗanda suka ƙware kuma suka karanci harkar kuɗi damar gudanar da aikin, yayin da shi kuma a ba shi matsayin da ya dace da fannin da ya karanta,” in ji ma’aikatan.

Sun ce ɗaukar irin wannan mataki zai tabbatar da adalci a Karamar Hukumar Musawa tare da inganta gudanar da ayyukanta.

Ma’aikatan sun kuma bayyana cewa akwai rashin jin daɗi da damuwa a tsakanin wasu ma’aikata kan wannan mataki, wanda suka ce zai iya yin tasiri ga yadda ake gudanar da ayyuka, tare da yiwuwar haifar da tasiri a harkokin siyasar yankin.

Jaridar Katsina Times ta yi ƙoƙarin jin ta bakin shugaban Karamar Hukumar Musawa kan zargin, amma bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba. Haka kuma, an tura masa saƙon rubutu, amma har zuwa lokacin kammala wannan rahoto bai bayar da amsa ba.

Jaridar ta kuma tuntubi kakakin Hukumar Kula da Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Jihar Katsina, Alhaji Bishir, wanda ya ce bai da masaniya kan wannan batu.

Sai dai ya shawarci duk wani ma’aikaci da ke da korafi kan wani ma’aikacin da aka tura masa wajen aiki da ya rubuta ƙorafinsa a hukumance.

Ya ce idan aka gabatar da korafin ta hanyar da ta dace, hukumomin da abin ya shafa za su saurari masu korafin tare da duba lamarin.

Katsina times 

@ www.katsinatimes.com 

Facebook page.katsina city news 

Facebook. Jaridar Taskar labarai 

07043777779

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 2 + 1?