Tubabbun ’Yan Bindiga Sun Halarci Bikin Naɗin Sarkin Ruman Katsina A Batsari

Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)Wasu daga cikin tubabbun ’yan bindiga da tsoffin jagororin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai sun fito daga daji, inda suka halarci bikin naɗin Sarkin Ruman…

Katsina City News August 30, 2026  ·  12:00 AM
| 40 Views
Tubabbun ’Yan Bindiga Sun Halarci Bikin Naɗin Sarkin Ruman Katsina A Batsari
Tubabbun ’Yan Bindiga Sun Halarci Bikin Naɗin Sarkin Ruman Katsina A Batsari



Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)


Wasu daga cikin tubabbun ’yan bindiga da tsoffin jagororin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai sun fito daga daji, inda suka halarci bikin naɗin Sarkin Ruman Katsina Hakimin Batsari, Alhaji Sani Tukur, a ranar Asabar, 29 ga Agusta, 2026.


Halartar tubabbun ’yan bindigar ya kasance ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi ɗaukar hankali a yayin bikin, wanda ya samu halartar al’ummar ƙaramar hukumar Batsari, sarakunan gargajiya, abokai, ’yan uwa da sauran masu fatan alheri daga sassa daban-daban na Najeriya.


An shirya gagarumin hawan daba da wasannin al’adu a yayin bikin, inda tubabbun ’yan bindigar suka fito fili suka bayyana goyon bayansu ga sabon Sarkin Ruma tare da jaddada muhimmancin zaman lafiya a Batsari.


Ɗaya daga cikin tubabbun, wanda ya bayyana sunansa da Tukur, ya nuna farin cikinsa kan abin da ya bayyana a matsayin sabon yanayin haɗin kai da fahimtar juna tsakanin al’umma da mutanen da a baya suke dauke da makamai.


Ya taya Masarautar Ruma murna, tare da bayyana Batsari a matsayin ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da suka samu ci gaba wajen samar da zaman lafiya a Jihar Katsina.


Shi ma Bala Musa, wanda aka ce ya yi suna a baya wajen ayyukan ’yan bindiga, ya halarci bikin, inda ya bayyana gamsuwarsa da irin zaman lafiyar da ake samu a yankin.


Ya ce fitowarsu daga daji domin halartar bikin sarautar na nuna irin ci gaban da aka samu wajen dawo da zaman lafiya da amincewa a tsakanin al’umma.


“Mun gamsu da zaman lafiyar da ake samu a Batsari, kuma ba mu da wata fargaba. Muna yi wa sabon sarki fatan alheri, muna roƙon Allah Ya ci gaba da jagorantar sa bisa gaskiya da adalci,” in ji Bala Musa.


Da yake tsokaci kan wannan ci gaba, Dakta Sada Salisu Ruma (Danwairen Katsina) ya bayyana taƙaitaccen tarihin sarautar Ruma tun daga zamanin Danwaire.


Ya ce bikin ya nuna sabon salon haɗin kai da sulhu a Batsari, yana mai bayyana cewa tubabbun ’yan bindigar sun kawo gudunmawar shanu, fura da nono mai yawa domin nuna goyon bayansu ga sabon sarki da ƙoƙarin samar da zaman lafiya.


Advertisement

NRS Gateway

Shi ma Mamman Mannir Murtala, shugaban Kwamitin Sasanci da Zaman Lafiya na Ƙaramar Hukumar Batsari, ya bayyana gamsuwarsa da yadda aka gudanar da bikin.


Ya ce halartar tubabbun ’yan bindigar da kuma gudunmawar da suka bayar na daga cikin alamomin da ke nuna ci gaban da ake samu wajen tabbatar da zaman lafiya.


“Kun ga tubabbun ’yan bindiga sun kawo mana nono, madara da shanu, yayin da ake gudanar da wasannin al’adu,” in ji shi.


Murtala ya ce tushen zaman lafiyar Batsari shi ne gaskiya, amana da gina kyakkyawar alaƙa tsakanin al’umma.


“Sirrin da muke takama da shi shi ne gina yarda da amana a tsakaninmu,” ya bayyana.


Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah ta Fulani, Hamisu Haruna, ya gode wa Allah bisa abin da ya bayyana a matsayin sabon haɗin kai tsakanin al’ummar Batsari da Fulani da ke zaune a daji.


Ya ce ranar ta kasance tarihi da ba a taɓa ganin irinta ba a yankin.


Shi ma Birgediya Janar Sagir Musa, wanda ya halarci bikin, ya yaba da yadda aka tsara taron, tare da yi wa sabon Sarkin Ruma da al’ummar Batsari fatan alheri.


A nasa jawabin, sabon Sarkin Ruman Katsina Hakimin Batsari, Alhaji Sani Tukur, ya bayyana godiyarsa ga Mai Martaba Sarkin Katsina da Masarautar Katsina bisa tabbatar masa da sarautar.


Ya kuma gode wa Gwamnatin Jihar Katsina, ’yan Majalisar Dokokin jihar, al’ummar Batsari da sauran jama’a daga ciki da wajen jihar bisa halartar bikin da nuna masa ƙauna da goyon baya.


Sarkin ya kuma yaba wa iyalansa, ’yan uwansa, abokai da sauran masu fatan alheri bisa irin goyon baya da kauna da suka nuna masa.


Fitowar tubabbun ’yan bindigar daga daji domin halartar bikin naɗin sarautar na ƙara jawo hankali kan ƙoƙarin sulhu da samar da zaman lafiya a Batsari, yankin da ya shafe shekaru yana fuskantar matsalolin tsaro.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 2 + 8?