Daga Mu'azu Hassan @ Katsina Times
Jaridar Weekend Trust ta ranar Asabar, 25 ga Yuli, 2026, ta wallafa rahoto kan yadda 'yan bindiga ke gallaza wa al'ummomin wasu yankuna a Jihar Neja, musamman a ƙananan hukumomin Borgu, Mariga, Shiroro da sauran wurare.
A cewar rahoton, 'yan bindigar sun kakaba wa mazauna yankunan haraji na kuɗi, wanda dole ne su biya kafin a bar su su zauna lafiya tare da gudanar da ayyukan noma a garuruwansu.
Wasu daga cikin mazauna yankunan da jaridar Daily Trust ta tattauna da su sun bayyana cewa, baya ga harajin kuɗi, 'yan bindigar sun sanya wasu tsauraran sharuɗɗa. Sun ce a duk lokacin da 'yan bindigar suka ga dama, suna shiga ƙauyukan su tare da kutsa kai cikin gidajen jama'a domin yi wa mata fyade.
Mazaunan sun ƙara da cewa, a wasu lokuta ma, 'yan bindigar kan tilasta wa wasu maza su kai musu matansu zuwa cikin daji, inda ake cin zarafinsu ta hanyar fyade kafin daga bisani a mayar da su gida.
Sun bayyana cewa wannan ne halin da sukke ciki a yanzu, lamarin da ya jefa al'ummomin yankunan cikin tsananin tsoro da rashin walwala.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Facebook page: katsina city news
Facebook page .jaridar taskar labarai


Comments (0)
No comments yet. Be the first to share your thoughts!