Alhaji Ibrahim Shema CON Ya Kaddamar da Cibiyar Tinubu/Dikko Women & Youth Centre, Ya Sanar da Shugabanninta

Daga Mu'azu Hassan, Katsina TimesTsohon Gwamnan Jihar Katsina kuma Sarkin Fulani, Alhaji Ibrahim Shehu Shema, ya kaddamar da sabuwar cibiya mai suna Tinubu/Dikko Women & Youth Centre, mai taken "Tinubu…

Katsina City News July 15, 2026  ·  12:00 AM
| 13 Views
Alhaji Ibrahim Shema CON  Ya Kaddamar da Cibiyar Tinubu/Dikko Women & Youth Centre, Ya Sanar da Shugabanninta
Alhaji Ibrahim Shema CON Ya Kaddamar da Cibiyar Tinubu/Dikko Women & Youth Centre, Ya Sanar da Shugabanninta

Daga Mu'azu Hassan, Katsina Times

Tsohon Gwamnan Jihar Katsina kuma Sarkin Fulani, Alhaji Ibrahim Shehu Shema, ya kaddamar da sabuwar cibiya mai suna Tinubu/Dikko Women & Youth Centre, mai taken "Tinubu da Dikko a  2027."

An gudanar da bikin kaddamar da cibiyar ne a ranar Talata, 14 ga Yulin 2026, a babban ofishin cibiyar da ke kan Titin Daura a cikin birnin Katsina. Taron ya fara da misalin karfe 11:00 na safe, inda ya gudana har zuwa kusan karfe 2:00 na rana.

Manyan jiga-jigan jam'iyyar APC da na gwamnati daga sassa daban-daban na Jihar Katsina ne suka halarci taron. 

Daga cikinsu akwai Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, PhD, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, MP, Shugaban Jam'iyyar APC na Jihar Katsina, Dr. Bashir Gambo Saulawa, tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Tukur Ahmed Jikamshi, fitaccen attajirin jihar, Alhaji Dahiru Barau Mangal, da sauran manyan jami'an gwamnati, masu takara , zababbun shugabanni da kuma dimbin magoya bayan jam'iyyar APC.


Bayan jawabai daga manyan baki da kuma wakokin fadakarwa da suka karfafa gwiwar magoya bayan APC, an sanar da jerin


 shugabannin cibiyar kamar haka:

Alhaji Salisu Yusuf Majigiri – Babban Darakta Janar.

Hon. Bashir Tanimu Dutsinma – Sakatare.

Hon. Ibrahim Lawal Dankaba – Shugaban Tsare-tsare.

Hon. Abdulwahab Sani Store – Sakataren Gudanarwa.

Alhaji Yusuf Shehu Shema – Mai Kula da Kyautatawa.

Hon. Jamilu Sadauki Dutsinma – Sakataren Kudi.

Advertisement

BSIL Security Report

Hon. Ahmed Danbaba Batsari – Mai Ba da Shawara kan Harkokin Shari'a.

Alhaji Rabiu Gambo Bakori – Shugaban Shiyyar Funtua.

Alhaji Abubakar Yusuf Bindawa – Shugaban Shiyyar Daura.

Alhaji Lawal Mai Iyali Dan Musa – Shugaban Shiyyar Katsina ta Tsakiya.

Sauran mambobin kwamitin gudanarwar cibiyar sun hada da Hon. Abdulhadi Abdullahi Kankara, Hon. Idris Yakubu Danchafa (Jibia), Hon. Lawal Audu Kankara, da Hon. Salisu Gambo Kaita.

Haka kuma, Mista Wale an nada shi a matsayin Daraktan Watsa Labarai, yayin da Hon. Mustapha Halilu Dutsinma ya zama Shugaban Matasa na cibiyar.

A bangaren mata kuwa, an nada:

Hajiya Binta Ado Sandamu – Shugabar Mata ta Shiyyar Daura.

Hajiya Jari Yar'Adua – Shugabar Mata ta Shiyyar Katsina.

Hajiya Ramatu Shehu Bakori – Shugabar Mata ta Shiyyar Funtua.

A karshen taron, an kuma sanar da cewa an fitar da sunayen shugabannin cibiyar daga matakin kananan hukumomi, domin ci gaba da fadada ayyukan cibiyar a fadin Jihar Katsina.


Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 6 + 8?