TARIHIN SARAUTAR TURAKI A MASARAUTAR KATSINA.
- Katsina City News
- 16 Nov, 2024
- 224
Sarkin Katsina Muhammadu Korau (1348-1398) shine Sarkin Katsina Musulmi na farko, kuma shine Wanda ya Fara kawo tsarin Sarauta, a Masarautar Katsina. Sarautar Turakin Katsina tana daya daga cikin Tsarin Sarautu tun wancan Lokacin. Sarautar Turaki tana daya daga cikin Tsarin Sarautu na Buwarorin Sarkin Katsina. Ayyukan Turaki sun hada da.
1. Turaki shine shugaban Buwarori a Masarautar Katsina, Buwarori sun hada da Tarno, Ajiya, Baraya, shamaki, Kilishi da sauransu.
2. Yana daya daga cikin aikin Turaki yin Wakilci idan wani Hakimi ya rasu, ko an tsaida shi saboda wata matsala. To ana tura Turaki ya rike Kasar Hakimin kamin a nada wani.
3. Idan kuma Sarki yana son ganin wani Mutum ko wasu mutane zai sanar da Turaki, shi kuma ya sanar da wadannan mutanen. Shiyyasa akeson gidan Turaki ya Zama kusa da Gidan Sarki, don aikin shi baya da kayyadaden lokaci.
4. Hakanan kuma Sarki yakan aiki Turaki acikin Kasar shi, ko wurin wani Sarki na wata Kasa akan wata magana ta tsakanin su ko daurin aure, ko murna ko taaziyya. Da dai sauransu.
A lokacin mulkin Dallazawa akwai Gidaje kamar guda biyu da sukayi riki wannan Sarauta ta Turakin Katsina. Akwai Gidan Turaki Agawa( BADAWA) akwai Gidan Tarno Abdullahi Barka ( Barebari).
Zuruar Badawan Katsina sune suka Fara wannan Sarauta ta Turakin Katsina a lokacin mulkin Sarkin Katsina Saddiqu Dan Ummarun Dallaje a shekarar 1835. BADAWA sunzo Katsina daga Kasar Bade wadda take Jihar Yobe ta yanzu, a lokacin mulkin Ummarun Dallaje a shekarar 1821. Mutum na farko da aka Fara nadawa Turaki daga cikin Zuruar Badawan Katsina shine:.
1. TURAKI MUHAMMADU DAWAI. Wanda Sarkin Katsina Saddiqu ya nadashi acikin shekarar 1835. Turaki Muhammadu DAWAI shine babban Dan Jagoran BADAWA Muhammadu Dogo. An haifeshi a Gorgoram cikin Kasar Bade. Yana daya daga cikin wadanda sukayima mahaifin shi rakiya daga Bade zuwa Sokoto anso Tuta acikin shekarar 1821. Bayan rasuwar Sarkin Katsina Malam Ummarun Dallaje sai dansa Saddiqu ya gajeshi, ya Zama Sarkin Katsina acikin shekarar 1835, sai ya nada Muhammad DAWAI Turakin Katsina. Bayan rasuwar Saddiqu sai danuwansa Muhammadu Bello ya gajeshi ya Zama Sarkin Katsina. Shi kuma Turaki Dawai sai yayi murabus daga Sarutar Turaki, yace aba kanensa Turaki Agawa.
2. TURAKI AGAWA. Sarkin Katsina Muhammad Bello shine ya nada Turaki Agawa acikin shekarar 1861. Lokacin da Turaki Agawa ya samu Sarautar Turaki yana zaune a Rimin BADAWA tareda Yan uwanshi to amma ranar da aka nadashi Turaki Sai Sarkin Katsina Muhammadu Bello ya sanar dashi cewa aikin Turaki na dare da rana ne bashi da kayyadaden lokaci, saboda haka ya dawo cikin gida Kofar soro da Zama, Turaki ya taso da gaba dayan zuruarshi daga Rimin BADAWA ya dawo Kofar soro da Zama acikin shekarar 1861. Wannan shine dalilin zuwan BADAWA Kofar soro. Daga cikin zuruar Turaki Agawa akwai. 1. Late Alhaji Mamman Agawa 2. Late Alhaji Mamman Dawai Katsina. 3. Late Alhaji Abu Yaro. 4. Alhaji Abu Bazariye ( Former Chairman TRCN) 5. Engineer Iro Gambo Former Director VR, INEC. 6. Alhaji Ibrahim Sayyadi ( Former Secretary to the Katsina State Government). 7. Alh. Musa Gambo Kofar soro( Chief Admin Officer, INEC Kano State) da sauransu. Daga Turaki Agawa sai
3. Turaki Ladan. Turaki Ladan yana daga cikin BADAWA da sukayi Sarautar Turaki. An nadashi Turaki a lokacin Sarkin Katsina Abubakar acikin shekarar 1904. Yayi Sarautar Turaki daga shekarar 1904-1921. Ya rasu a Saudiyya a shekarar 1921, lokacin da suka aikin Hajji na farko tare da Sarki Dikko. Daga Nan sai aka nada kanen mahaifin shi watau
4. TURAKI USMAN JARI. Yayi Turaki daga shekarar 1930-1933. Daga shi sai
5. TURAKI SULE BAWA (1933-1963). Turaki SULE shine Turaki na karshe daga cikin zuruar BADAWA da suka rike Sarautar Turaki. Ya rasu acikin shekarar 1963.
Daga Nan sai Sarautar ta koma Gidan Tarno Abdullahi Barka. Tarno Barka mutumin Kasar Borno ne ( Babarbare). Yazo Katsina alokacin mulkin Dallazawa. Daga cikin zuruar Tarno da sukayi Turaki akwai:
1. Alhaji Isiyaku. Alhaji Isiyaku Turaki an nadashi Turaki alokacin Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo. Daga cikin zuruar Alhaji Isiyaku akwai 1. Late Alhaji Sani Store 2. Senator Abba Ali 3. Alhaji Usman Isiyaku ( Tarno) da sauransu. Bayan Alhaji Isiyaku ya rasu sai aka nada dansa watau
2. TURAKI SANI STORE. Daga cikin zuruar Turaki Sani akwai. 1. Lawal Sani Store 2. Abdulazeez Sani Store. 3. Dr. SULE Sani da sauransu. Bayan rasuwar Sani Store sai kuma aka nada
3. Dr. SULE Sani a matsayin Turakin Katsina. Bayan rasuwar sa sai aka nada
4. SENATOR ABBA ALI. Abba Ali shekarar shi daya bisa sarautar ya rasu a Saudiyya. Sai aka nada
5. Alhaji Lawal Sani Store. Wanda har ya zuwa yanzu shine Turakin Katsina.
Alh. Musa Gambo Kofar soro.