Ko kun san asalin “Sai-Baba-ta-gani”?
- Katsina City News
- 13 Mar, 2024
- 780
Kalmar Sai-Baba-ta-gani ta shiga bakin al’umma musamman a wannan zamani na yawaitar yajin aikin ‘yan kwadago. Amma kun san yadda ta samu shiga harshen Hausa?
Ku karkade kunnawanku ku ji tarihin wannan batu kamar yadda Jarman Kano Isah Hashim ya shaidawa marigayi Tijjani Ado Ahmad, mai gabatar da shirin Barka da hantsi na Freedom Radiyo Kano.
Tushen maganar dai ya taso ne daga zamanin yakin duniya na biyu, wanda Hausawa ke kira yakin Hitila ko yakin Burma.
Da yake a shekarun yakin, 1939-45, Najeriya na karkashin mulkin Burtaniya sai Turawa suka yi ta yada farfaganda don neman matasa da za su shiga aikin soja.
Daya daga cikin farfagandar da aka yada a lokacin, ita ce cewar duk wanda ya je yaki ya dawo za’a nada shi sarkin garinsu.
Hakan ta sa matasa da dama su ka yi ta shiga aikin soja saboda kwadayin sarauta. Amma inda gizon ke saka shi ne, matasan arewacin Najeriya da dama sai su ka fi sha’awar a nada su sarkin Kano maimakon sarakunan garinsu. Don haka masu irin wannan kudirin sai su ka yi ta shiga aikin soja da sunan mutanen Kano. Sai ka ga Ali Kano, Idi Kano, Mamman Kano amma ko ‘zo nan’ basa ji a harshen Hausa.
Bayan dawowa daga yaki, sai Turawa suka maye gurbin wacce farfagandar karya da samawa wadanda su ka dawo aikin ‘yan doka. To wadannan ‘yan doka marasa Hausa da suka kama aiki a Kano sai Allah ya yi su, masu gaskiya ne da rashin karbar cin hanci.
Saboda haka duk lokacin da suka kama mai laifi, in ya fara ba su hakuri ko ya yi yunkuri ba da na goro, sai su cukuikuye shi su ce ‘sai-Baba-ta-gani’. Ma’anarsu, ba za su sake shi ba sai wakilin doka – wanda su ke kira Baba – ya gan shi kuma ya dauki mataki a kansa.
Daga nan harshen Hausa ya karu da Sai-Baba-ta-gani, wato ba zamu bari ba sai mai iko a kan lamarin ya Gani.