Kama Dakta Bashir Kurfi: Ranar Kuskure Ba A Dai-Dai!!!Me ya kawo "yan siyasar adawa?

Daga Aliyu Abdulhadi, PhDNa kalli hirar da Dakta Bashir Kurfi ya yi da Trust TV, wadda aka wallafa a YouTube. A ganina, duk wanda ya saurari hirar cikin natsuwa abin…

Katsina City News July 11, 2026  ·  12:00 AM
| 24 Views
Kama  Dakta Bashir Kurfi: Ranar Kuskure Ba A Dai-Dai!!!Me ya kawo "yan siyasar adawa?
Kama Dakta Bashir Kurfi: Ranar Kuskure Ba A Dai-Dai!!!Me ya kawo "yan siyasar adawa?

Daga Aliyu Abdulhadi, PhD

Na kalli hirar da Dakta Bashir Kurfi ya yi da Trust TV, wadda aka wallafa a YouTube. A ganina, duk wanda ya saurari hirar cikin natsuwa abin da zai iya cewa shi ne: "Ranar kuskure ba a dai-dai."

Kafin wannan hira, Dakta Kurfi ya taba yin wata hira bayan taron da suka gudanar a Katsina, wanda wasu 'yan daba suka tarwatsa. A wancan lokacin ma ya yi wasu zarge-zarge, amma gwamnati ba ta dauki wani mataki a kansa ba.

A ganina, kuskuren farko shi ne, ya kamata Dakta Kurfi ya fahimci cewa shi dan gwagwarmaya ne, malamin jami'a ne, kuma mutum ne da ke cikin siyasa. Saboda haka, duk wata magana da zai furta ya kamata ta kasance mai tushe, mai hujja kuma ta dace da matsayinsa.

Sai dai a wannan hira, ya yi kalamai cikin azarbabi tare da gabatar da wasu zarge-zarge da ba a ga hujjojin shari'a da suka tabbatar da su ba. A maimakon haka, sun yi kama da bayanan da ake tattaunawa a wuraren zaman shan shayi.

Abu na biyu kuwa shi ne batun tsaro musamman wanda ya shafi ayyukan ta'addanci da 'yan bindiga. Wannan lamari ne mai matukar muhimmanci da ba a wasa da shi a Najeriya. 

A baya an gayyaci fitattun mutane domin amsa tambayoyi kan irin wadannan batutuwa. Misali, Janar TY Danjuma ya taba zargin cewa wasu jami'an tsaro na hada kai da 'yan bindiga, lamarin da ya jawo kira a gayyace shi domin karin bayani. Haka kuma, an taba cire Gwamna Joshua Dariye daga mukaminsa bisa wasu batutuwan tsaro. Don haka, batun tsaro ba karamin al'amari ba ne.

Abu na uku shi ne yadda shugabannin jam'iyyun adawa suka shiga cikin lamarin. A ganina, hakan ya kara rikita al'amarin maimakon a mayar da hankali wajen nemo mafita. Tunda kuskure ya faru, abin da ya fi dacewa shi ne a nemo hanyar sasanci da warware matsalar.

Advertisement

BSIL Security Report

Na farko da ya yi magana shi ne Ahmed Babba Kaita, dan takarar gwamna na jam'iyyar ADC. Daga baya kuma Mustapha Inuwa na bangaren PDP mai biyayya ga Tanimu Turaki, sai Sanata Yakubu Lado na bangaren PDP mai alaka da Nyesom Wike. Haka kuma wasu dattawan Katsina da suka yi magana, idan aka duba, galibinsu suna da alaka da jam'iyyun adawa.

Wannan ya sa wasu daga bangaren gwamnati, jam'iyya mai mulki da kuma masu goyon bayan gwamnati da wasu yan gwagwarmayar na hakika ,suka fara tambayar ko akwai wata alaka tsakanin Dakta Kurfi da jam'iyyun adawa. Hakan ya kuma jawo muhawara a kafafen sada zumunta kan ko su ne ke amfani da shi wajen sukar gwamnatin Katsina.?!

Rahotannin da wasu kafafen yada labarai suka wallafa sun nuna cewa daya daga cikin dalilan da suka sa ba a ba Dakta Kurfi beli a zaman farko shi ne rashin rubuta bayaninsa ga 'yan sanda cikin lokaci. Idan hakan ya tabbata, wannan ma wani kuskure ne daga bangaren shi.

Wata tambaya kuma ita ce: Mene ne laifin gwamnati idan ta ba da dama a janye kalaman ko kuma a warware matsalar kafin ta kai kotu, amma hakan bai faru ba? A irin wannan yanayi, gwamnati na iya ganin cewa dole ta bi hanyar doka domin kare martabarta. Idan ba ta yi hakan ba, ana iya ci gaba da amfani da lamarin wajen yi mata suka, musamman yayin da ake shirin shiga kakar zabe.

Shawarata ita ce;

idan da gaske ana son taimakawa Dakta Kurfi, ya dace wasu dattawa masu mutunci da kima su shiga tsakani domin neman afuwa, tattaunawa da kuma samar da mafita cikin lumana.

Sai dai idan aka yi la'akari da abin da ke cikin bidiyon hirar, a ganina, ranar kuskure ba a dai-dai.

Aliyu Abdulhadi, PhD, malamin jami'a ne kuma memba ne na Kungiyar Marubuta ta Kasa (ANA), reshen Abuja.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 5 + 6?