Daga Comrade Sabi’u Idris Yamel
Coordinator, K7 Grassroots Movement
A yau, duk wata al’umma da ke son ci gaba dole ne ta fara da ilimi, domin ilimi shi ne ginshiƙin da ke haifar da shugabanni, ƙwararru, da matasa masu hangen nesa.
Wannan fahimta ce da Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura ya ɗauka da muhimmanci tun bayan da al’ummar Daura suka ba shi amanar wakilcinsu a Majalisar Dokokin Jihar Katsina.
A cikin ɗan lokaci da ya shafe yana wakilci, ya mayar da hankali sosai wajen bunƙasa ilimi a matakai daban-daban, musamman ga matasa. Daya daga cikin manyan matakan da ya ɗauka shi ne ƙaddamar da shirin cikakken tallafin karatu (Fully Funded Scholarship Scheme) ga ɗalibai sama da 700 da ke karatu a jami’o’i, kwalejojin ilimi, kwalejojin kiwon lafiya, kimiyya da fasaha.
Wannan tsari, yana ɗaukar nauyin ɗalibi tun daga farkon shigarsa makaranta har zuwa kammala karatunsa.
Wannan yana nufin an cire babban ƙalubalen kuɗi daga kan matasa da dama, domin su mayar da hankali kan karatu da gina makomarsu.
Tasirin Wannan Shirin ya riga ya fara bayyana ta hanyar yadda ɗalibai ke samun damar ci gaba da karatunsu cikin kwanciyar hankali da natsuwa.
Baya ga wannan, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura ya kuma gina da bunƙasa Islamiyyoyi a sassa daban-daban na Daura, ya tallafa wa cibiyoyin ilimi ta hanyar gyara wuraren karatu, ya biya wa ɗalibai kuɗin jarabawar SSCE , samar da uniform da littafai ga 'yan firamare, ya taimaka wa ɗaliban manyan makarantu wajen biyan kuɗin rajista, sannan ya samar da guraben aiki da tallafin rayuwa ga matasan da suka kammala karatu.
Dukkan waɗannan suna nuna cewa ba ya kallon ilimi a matsayin taimako na wucin gadi, sai dai a matsayin zuba jari na dogon lokaci domin gina al’umma mai ƙarfi da ilimi.
A matsayin mu na matasan K7 Grassroots Movement, muna da yaƙinin cewa wannan hangen nesa na ilimi zai ƙara faɗaɗa tasirinsa idan aka ba Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura damar wakiltar Shiyyar Daura a Majalisar Dattawa.
Domin a fili yake cewa duk al’ummar da ta zuba jari a ilimin matasanta, ta riga ta gina makomarta.
Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura ya zaɓi hanya mafi muhimmanci: hanyar gina ɗan Adam.
Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura Jagoran da ya mayar da ilimi ginshiƙin ci gaban matasa domin inganta makomar Daura Zone.
#K7GrassrootsMovement
#NasirYahayaDaura2027
#DauraZone
#IlimiTushenCiGaba
#ScholarshipForDevelopment