Kachalla Muhammadu Ne Ke Riƙe da Rabe Abubakar — Binciken Jaridun Katsina Times

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes31052026_122656_FB_IMG_1780230357400.jpg



Daga Binciken Jaridun Katsina Times, Majiyoyi daban-daban sun tabbatar wa da Jaridun Katsina Times cewa Manjo Janar mai ritaya, Rabe Abubakar, wanda wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi a ranar Asabar, 30 ga watan Mayu, yana hannun wani fitaccen jagoran ’yan bindiga a yankin Matazu mai suna Kachalla Muhammadu.

Majiyoyin sun bayyana cewa wasu ’yan bindiga da aka fi sani da KB ne suka kai harin a wani wuri kusa da ƙauyen Zakin Baure, da ke kusa da garin Matazu, inda suka yi awon gaba da Rabe Abubakar tare da matarsa.

A cewar majiyoyin, waɗanda suka sace su ba su san ko wanene Rabe Abubakar ba a lokacin da suka kai harin. Sun dai kai harin ne da nufin kama wani babban jami’in gwamnati ko wani attajiri domin neman kuɗin fansa.

Rahotanni sun ce bayan ƙungiyar KB ta kama shi, sai aka miƙa shi ga Kachalla Muhammadu, wanda a yanzu ake zargin yana tsare da shi a maboyarsa.

Kachalla Muhammadu matashi ne mai shekaru kasa da 30, ɗan ƙaramar hukumar Matazu ne daga gundumar Sayaya. Ya fito ne daga wata ruga da ake kira Kogon Maidawa, inda har yanzu iyayensa da sauran danginsa ke zaune.

A baya, Kachalla Muhammadu na daga cikin waɗanda suka amince da yarjejeniyar sulhu tsakaninsu da gwamnati. A cikin wani sautin murya da ya taɓa yawo a kafafen sada zumunta, ya bayyana cewa tun bayan rungumar sulhu yake ƙoƙarin kare al’ummomin ƙananan hukumomin Matazu, Musawa, Kankia da kuma Charanchi daga hare-haren ’yan bindiga.

A cikin wannan sautin, ya kuma bayyana cewa ya fara nuna rashin gamsuwa da sulhun ne bayan wasu sojoji daga Jihar Kano sun kai samame kasuwar Jikamshi, inda suka kama wasu daga cikin mutanensa tare da kwashe shanunsa. Ya yi zargin cewa ba a dawo masa da mutanensa ko dabbobinsa ba duk da ƙoƙarin da ya yi.

Majiyoyi sun ce an gudanar da wannan samamen sojojin ne ba tare da sahalewar jami’an tsaro ko gwamnatin Jihar Katsina ba.
Tun daga wannan lokaci ne, a cewar majiyoyin, Kachalla Muhammadu ya koma kai hare-hare masu muni a yankin. Ana zarginsa da kai hari garin Jikamshi, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayukan mutane da dama.

Majiyoyinmu sun tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa da Kachalla Muhammadu domin ganin an sako Manjo Janar mai ritaya Rabe Abubakar cikin koshin lafiya.

Haka kuma, majiyoyin sun ce tun bayan wannan hari da sauran matsalolin tsaro da ake fuskanta a yankin, jami’an gwamnatin Jihar Katsina suna ci gaba da ɗaukar matakai da gudanar da tuntuba domin magance matsalolin tsaro da kuma tabbatar da dawo da zaman lafiya.

Follow Us