Daga Garba Abu Abdullahi Jikamshi
Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bukaci gwamna Abba Kabir Yusuf da ya dauki matakin da ya dace a kan ma su yi wa gwamnatin sa wani gani-gani.
Sarki Sanusi ya bayar da shawarar ne a lokacin da ya Kai gaisuwar Sallah ga gwamnan na jihar Kano, kamar yadda ya ke bisa al'ada.
Sarkin na Kano ya yi nuni da cewa wajibi ne a rika hada adalci da kuma karfin Iko a sha'anin shugabanci, in dai har a na son ganin daidai.
Ya yabawa Abba Kabir Yusuf a bisa fadada shirye-shiryen kiwon lafiya da makarantu da matakan kyautatawa al'umma, sai dai Kuma ya yi gargadi a kan girmama mutanen da ba su cancanta ba.
Sarki Muhammadu Sanusi ya ce a yanzu mutane su na dauka akwai Gwamna Mai matukar hakuri da kawaici, don haka kowa na iya yin abinda ya ga dama.
A yayin da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ke mayar da jawabi, ya godewa Sarkin a bisa ziyarar, ya na mai bayar da hakuri a kan soke hawan Daushe.
Gwamna Abba Kabir ya kara da cewa tun daga ranar da Allah Ya nufe shi da zama Gwamna, bai taba shakka ko tsoron wani Dan Adam ba, face Ubangiji.