Daga Mu’azu Hassan
Har zuwa daren Lahadi, 24 ga Mayu, 2026, jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Katsina ba ta cimma matsaya kan wanda zai zama ɗan takararta na gwamna ba.
Majiyoyi daban-daban daga cikin jam’iyyar sun tabbatar wa da Katsina Times cewa ’yan takara guda biyar sun kasa cimma matsaya bayan doguwar tattaunawa da suka gudanar har zuwa daren Lahadi.
Bayan gaza cimma yarjejeniya, ’yan takarar sun amince da dage ci gaba da neman mafita har sai bayan bukukuwan Sallah, la’akari da cewa yau Litinin za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, Talata kuma ranar Arfa ce, yayin da Laraba za a yi Sallah.
’Yan takarar da ke neman tikitin gwamnan sun haɗa da Saddiq Yar'Adua, Mustapha Inuwa, Ahmed Babba Kaita, Ahmed Aminu Yar'Adua da kuma Lawal Daura.
Majiyoyinmu sun bayyana cewa wani kwamiti na mutum shida ya bayar da shawarar a mayar da takarar zuwa shiyyar Daura, lamarin da ya bai wa mutum biyu damar tattaunawa domin su daidaita tsakaninsu. Mutanen biyu su ne Ahmed Babba Kaita da Lawal Daura. Sai dai sun kasa cimma matsaya.
Rahotanni sun nuna cewa sauran ’yan takara uku sun yi watsi da tsarin, suna masu cewa ba tsarin dimokuraɗiyya ba ne kuma bai dace da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ADC ba.
Daga bisani, kwamitin ya sake fito da wani tsari na tantance ’yan takarar tare da ba su maki da matsayi, inda aka bayyana cewa Lawal Daura ne ya fi cancanta ya zama ɗan takara.
Sai dai sauran ’yan takarar sun yi fatali da wannan matsaya, suna masu cewa ta saɓa wa dokokin Independent National Electoral Commission (INEC), saboda haka aka yi watsi da ita nan take.
Jam’iyyar ADC ta bar ’yan takarar su ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu domin neman maslaha, amma hakan bai haifar da matsaya ba har zuwa tsakar daren Lahadi.
Binciken Katsina Times ya nuna cewa a tsakanin tsofaffin ’yan siyasa da mutanen gari, Saddiq Yar'Adua ne ke da mafi yawan goyon baya, yayin da Mustapha Inuwa ke biye masa.
Haka kuma, a tsakanin tsofaffin ’yan boko da tsofaffin jami’an tsaro, mutane da dama na nuna goyon baya ga Lawal Daura.
Rahoton binciken ya kuma nuna cewa wasu kalaman da Ahmed Babba Kaita ya taba furtawa a baya suna ci gaba da yi masa illa a tsakanin wasu ’yan siyasa, duk da cewa yana da karɓuwa sosai a tsakanin wasu masu amfani da kafafen sada zumunta.
A bangaren Ahmed Aminu Yar'Adua kuwa, masu sharhi na ganin siyasar sa ba ta cika bayyana ba sai lokacin zaɓe.
A halin yanzu, ADC a Katsina na da ɓangarori biyu. Bangaren Musa Wamba ya riga ya fitar da nasa ɗan takara, wato Salisu Uli, tsohon sakataren jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma tsohon shugaban riƙo na PDP.
Uli ya shaida wa jaridun Katsina Times cewa ya sayi fom ɗin takara kuma shi ne zai tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar ADC ba tare da wata hamayya ba.