NAJERIYA ZA TA BIYA KUDIN RUWA DALA BILIYAN 11 NA BASUSSUKA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes14052026_223933_FB_IMG_1778798323698.jpg

Daga Garba Abu Abdullahi Jikamshi 

Shugaban Kasar Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa Najeriya za ta biya jimlar Dala biliyan 11 da miliyan 600 a matsayin kudin ruwa na basussukan da ta ciwo.

A cewar shugaban na Najeriya, za a biya kudin ruwan ne a cikin shekara ta 2026

Ya Kuma kara da cewa gwamnati ta bunkasa bangaren bankuna na kasa, Wanda a yanzu haka su na da jarin da ya ke da karfin dala biliyan uku da miliyan 400.

Shugaba Tinubu ya ce wannan ya fitar da Najeriya daga cikin jerin kasashen da Hukumar Tsara Hada-hadar Kudade ta Kasa da Kasa wato FATF ke da fargaba a kan su.

Shugaban Najeriya dai ya bayyana hakan ne a birnin Nairobi na Kenya, a yayin wani babban taro.

Follow Us