Gwamna Raɗɗa Ya Kaddamar da Motoci ga Hukumar KASSAROTA Domin Inganta Tsaron Hanya a Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes07052026_144439_FB_IMG_1778165027730.jpg



Daga Katsina Times

Gwamnan Jihar Dikko Malam Dikko Umar Radda, a ranar Alhamis, ya kaddamar da motoci ada gwamnatin jihar Katsina ta samar wa Hukumar Kula da Tsaro da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Katsina (KASSAROTA), domin kara inganta ayyukan kula da zirga-zirga da tsaron hanya a fadin jihar.

An gudanar da bikin kaddamarwar ne a harabar gidan gwamnatin jihar Katsina Muhammadu Buhari House.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da shugabannin hukumar KASSAROTA karkashin jagorancin babban daraktan Hukumar Manjo Garba Yahaya Rimi, mai ritaya, da babban kwamandan hukumar Dahiru Mani Bagiwa (rtd) da sauran jami’an hukumar.

Da yake jawabi yayin kaddamarwar, Gwamna Raɗɗa ya ce samar da motocin aikin na daga cikin kudurin gwamnatinsa na inganta tsaron hanya, kula da zirga-zirga da kuma ayyukan ceto a fadin jihar.

Ya bayyana cewa motocin za su taimaka wajen kara wa jami’an KASSAROTA karfin gudanar da ayyukansu, musamman wajen tabbatar da bin dokokin hanya, dakile hatsurran mota da kuma saurin kai dauki a lokuta daban-daban.

Gwamnan ya jaddada muhimmancin ingantaccen tsarin kula da zirga-zirga wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da bunkasa harkokin tattalin arziki da zamantakewa.

Raɗɗa ya kuma yaba wa jami’an KASSAROTA bisa jajircewarsu wajen gudanar da aiki, tare da kira gare su da su ci gaba da nuna kwarewa, da’a da adalci yayin gudanar da ayyukansu.

Ya sake tabbatar da aniyar gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa hukumomin da ke kula da tsaro da zaman lafiya ta hanyar samar musu da kayan aiki da sauran bukatun gudanarwa.

A nashi jawabin, shugaban hukumar KASSAROTA ya gode wa gwamnatin jihar bisa wannan tallafi, yana mai bayyana motocin a matsayin babban ci gaba ga ayyukan hukumar.

Rimi ya kuma yi alkawarin kara kaimi wajen wayar da kan jama’a kan tsaron hanya, inganta kula da zirga-zirga da kuma kare masu amfani da hanyoyi a fadin jihar.

Follow Us