Daga Katsina Times
Gwamnatin jihar Katsina ta rattaba hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniya da kamfanin fasahar na Birtaniya, Conflow Power Group, tare da hadin gwiwar kamfanin Mora Energy na Najeriya, domin girka fitilun titi masu amfani da hasken rana guda 50,000 (iLamp) a fadin jihar.
Wannan shiri zai sanya Katsina zama jiha ta farko a Afirka da za ta kafa cibiyar bayanan ilimin na’ura mai kwakwalwa (AI) mai rarrabuwa a matakin jiha baki daya.
A cewar bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar, fitilun iLamp ba wai samar da hasken titi kawai za su yi ba, har ma za su rika aiki a matsayin kananan cibiyoyin tattara da sarrafa bayanan AI, tare da bayar da wasu muhimman ayyuka ga al’umma.
An bayyana cewa kowanne iLamp na dauke da fasahohin zamani da suka hada da kyamarori masu amfani da AI da tsarin sa ido, wanda ake sa ran zai taimaka wajen inganta tsaro, sarrafa zirga-zirga da kuma kare kadarorin gwamnati.
Haka kuma, ana sa ran tsarin zai samar da intanet kyauta (WiFi), fasahar Bluetooth da kuma hasken LED mai inganci, dukkansu suna aiki ne da hasken rana ba tare da karin nauyin kudin wutar lantarki ga gwamnati ba.
Masana sun bayyana cewa wannan sabon tsari ya bambanta da manyan cibiyoyin bayanan AI da ake ginawa a wasu kasashe, musamman a Amurka, inda ake fuskantar kalubale na yawan amfani da wutar lantarki da ruwa. A tsarin iLamp kuwa, ana amfani da hasken rana kacal, ba tare da bukatar wutar lantarki ta kasa ko ruwa domin sanyaya na’urori ba.
Da yake jawabi, Shugaban kamfanin Conflow Power Group, Edward Fitzpatrick, ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wani babban sauyi a fannin amfani da AI, yana mai cewa Katsina ce jiha ta farko a Najeriya da ta fara aiwatar da wannan tsari a irin wannan mataki.
Ya kara da cewa, girka fitilun iLamp 50,000 zai samar da karfin sarrafa bayanai mai yawa, tare da shirin kafa masana’antar farko ta kamfanin a jihar, wanda ake sa ran zai habaka samar da makamashi mai tsafta a Najeriya.
Shi ma Shugaban Mora Energy, Stanley Chuka-Umeora, ya ce aikin zai taimaka wajen kara tsaro a tituna, kawo fasahar AI kusa da jama’a, tare da daga darajar Najeriya a taswirar fasahar zamani a duniya.
A nasa bangaren, mai ba da shawara kan makamashi ga gwamnatin Katsina, Dr. Hafiz Ibrahim Ahmad, ya bayyana cewa shirin zai kawo sauyi mai ma’ana ga rayuwar al’umma, ciki har da inganta tsaro, rage laifuka, samar da intanet kyauta da kuma kara hanyoyin samun kudaden shiga ga jihar.
Rahotanni sun kuma nuna cewa ana shirin fadada aikin zuwa wasu sassa na Najeriya, inda ake hasashen girka sama da fitilun iLamp 300,000 a nan gaba, wanda zai zama mafi girman tsarin hadin gwiwar hasken titi da AI a nahiyar Afirka.
Bugu da kari, ana tattaunawa kan amfani da wannan fasaha a babbar hanyar Lagos zuwa Calabar mai tsawon kilomita 700.
Kamfanin Conflow Power Group, wanda ya samu lambar yabo ta duniya a shekarar 2026, ya shahara wajen kirkirar iLamp — fitilar titi mai aiki da kanta, mai samar da kudaden shiga, tare da dauke da na’urorin AI. Ana amfani da wannan fasaha a kasashe sama da 30 a duniya.