Daga Katsina Times | 11 ga Afrilu, 2026
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umurci manyan jami’an tattalin arzikin ƙasa da su gaggauta samar da matakan da za su rage tasirin rikicin Gabas ta Tsakiya da ke ci gaba da shafar tattalin arzikin Najeriya.
Tinubu ya bayar da wannan umarni ne a ranar Juma’a a Yenagoa, yayin wata liyafa da aka shirya bayan ƙaddamar da ayyukan ci gaba da gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ya aiwatar.
Sanarwar hakan na kunshe ne cikin wata takarda da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar.
Shugaban ya bukaci Ma’aikatun Kuɗi da Kasafin Kuɗi, tare da Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Misis Didi Esther Walson-Jack, da su lalubo hanyoyin rage matsin tattalin arziki da ke addabar ‘yan ƙasa.
Ya amince cewa rikicin na Gabas ta Tsakiya ya haifar da matsin lamba ga tattalin arziki, musamman ta fuskar hauhawar farashin mai, wanda ke tasiri kai tsaye ga rayuwar jama’a.
“Farashin mai yana da matuƙar tasiri, amma dole ne mu fuskanci gaskiyar halin da duniya ke ciki,” in ji Tinubu.
Ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta yi aiki tare da dukkan hukumomin da abin ya shafa domin samar da matakan rage wahalhalu.
Haka kuma, ya sake jaddada kudirin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na inganta walwalar al’umma ta hanyar shugabanci mai tasiri da kawo ayyukan more rayuwa.
A yayin ziyarar, shugaban ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka da suka haɗa da tashar wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 60 a Elebele, gadar Angiama-Oporoma mai tsawon mita 630, da sabuwar hanyar birnin Yenagoa.
Tinubu ya yaba da kokarin Gwamna Diri, yana mai cewa ayyukan sun dace da manufofin “Renewed Hope” kuma za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.
Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi wajen hanzarta ci gaba mai ɗorewa.
A nasa jawabin, Gwamna Diri ya ce goyon bayan gwamnatin tarayya ya taimaka wajen aiwatar da ayyukan samar da wutar lantarki da kuma ƙarfafa ‘yancin kai a fannin makamashi a jihar.
A ƙarshe, shugaban ya yi shiru na minti ɗaya domin girmama sojojin da suka rasu da kuma tsohon gwamnan Bayelsa, marigayi DSP Alamieyeseigha.
(NAN)