KatsinaTimes / Facebook Page: Katsina City News
Wani katafaren gini dake cikin birnin katsina da aka dade ana magana akansa shine wanda ke bisa titin IBB,bayan gidan Alhaji Abdu fari.kusa da shatale talen massalacin gidan AD saude.
Ginin anyi shi ..a Mazaunin tsohuwar tashar birnin katsina. Wanda aka tado tashar aka mayar da ita inda take a yanzu bisa titin zuwa Dutsinma.
An fara ginin faka faka a shekarar 1997.Aka kaishi matsayin da yake.Amma tunda aka tsaida ginin wasu sunce a shekarar 1998 wasu sun ce a 1999.aikin yayi tsaye cak ba gaba ba baya.
ME YA TSAIDA AIKIN?
Iya binciken mu, mun kasa samun wanda zai mana bayanin, akan me ya tsaida aikin.Amma akwai shaci fadi da muka ji.
Wasu sun ce da yake ginin yana. akan tsohuwar tashar katsina ne,ana zargin Ajannu suka hana karasa ginin.shi ya sa ma masu wannan ra ayin suke kiransa da ginin Aljannu.
Wasu kuma sunce, a lokacin ginin an samu wata matsala da wani makwabcin ginin.Har ta kai ga anyi sa in sa.makwabcin yace tun da aka shiga hakkin shi ,zai ga yadda za a kammala aikin.
Ana tsammanin shekaru 26 aka tsaida ginin har yanzu komi ya tsaya cak.
Tambayar da kowa a katsina ke maganar shi ,itace wa ya mallaki gidan nan?
Gini ne katafare da kamar wata cibiyar kasuwancin zamani? Amma me ya tsaida ginin?