Jam iyar ADC a jahar katsina ta bi umurnin kotu ...Hawan jini na shirin kama wasu 'ya'yanta.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes09042026_110523_IMG_20260409_104546_065.jpg

Daga Ahmad Muhammad @ KatsinaTimes

Binciken jaridun katsina times ya tabbatar da cewa jam iyyar ADC a jahar katsina tayi biyayya ga umurnin kotu na tsayar da duk ayyukan ta, har zuwa lokacin fara shari ar da shugaban ta Musa wamba ya shigar.
A tsarin jam iyyar a yau  Alhamis ya kamata, suyi zaben  shugabannin rumfunan da  zabe  shugabannin unguwanni da kuma na kananan hukumomi. 
Za kuma suyi na jaha inda za a zabi shugabannin jaha a ranar asabar mai zuwa.
Bincike katsina times ya gano duk wadannan zabubbukan basu gudana a yau.wakilan katsina times sun kewaya dukkanin ofisoshin ADC da ake dasu a katsina, sun ga babu kowa, ba alamar jam iyyar na shirin wani taro na zabubbuka.
Wakilan katsina times sun tuntubi wasu shugabannin ADC na unguwanni da na kananan hukumomi ko akwai wani shiri na zabubbukan da aka shirya yau..amsar da suka bamu shine suna jiran umurnin shugabannin su.
Daga abin da Wakilan mu suka gani da kuma ji shine jam iyar tabi umurnin da kotu ta bata na dakatar da komi.
Mun kasa samun wani jigo a jam iyar da zai mana bayani akan hakan.
BARAZANAR HAWAN JINI GA "YA "YAN TA.
Wani labari da jaridun times suka samu shine akwai damuwa da a tsakanin wasu da suka sadaukar suka kuma yima jam iyyar wahala.Amma yanzu an tsara shugabannin da zasu tafiyar da jam iyar an ki saka su.
Wasu da mukayi magana dasu da basu yarda a bayyana sunansu ba.sun bada misalin wata mata da ta kashe kudin ta ga jam iyyar amma yanzu an hana ta wani mukami da tayi fata kuma ta nema.
Wani matashi da ya bayyana irin sadaukarwa da ubangidan shi yayi amma yanzu an bar ubangidan nashi a tutar babu.
Wasu sun bayyana cewa fitar da shugabannin jam iyyar da wasu suka tsara shine zai tarwatsa jam iyar a jahar katsina. 
Wani yace hatta shi Wamba da ya kai kotu.sai da ya nemi ko za a chanza shi to a bashi wani mukami a kasa.Amma sai aka ce  a a a sai dai ya zama dan kallo.
"Da yawa na fama da Barazanar ciwon hawan jini " inji wani dan jam iyyar.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com 
Facebook page.katsina city news.
Facebook page. Jaridar taskar labarai 
Katsina times @ other social media handles 
07043777779.08057777762

Follow Us