@ katsina times
Wata kotu a jahar katsina karkashin mai shari a.A.K Tukur ta dakatar da duk wata hidima ta jam iyyar ADC ta jahar katsina,har sai ta kammala sauraren shari ar da aka shigar gaban ta, kuma ta saka ranar 15 ga watan afrilu a ranar da za a saurari karar da aka shigar.
Shugaban jam aiyyar ADC na jahar katsina.Alhaji Usman wamba shine ya shigar da karar ,inda yake karar Alhaji Lawal Batagarawa da Alhaji Babangida Ibrahim Mahuta da jam iyyar ADC da hukumar zabe ta kasa.Bisa wasu bukatu guda shidda.
Kotun ta amince da dukkanin bukatun har zuwa ranar 15 ga watan afrilu lokacin da zata fara sauraren karar.
Jam iyyar ADC ta tsara fara tarurrrukan ta daga ranar alhamis mai zuwa ..zuwa ranar asabar da zata yi babban taron ta da zaben sabbin shugabannin jaha.Da wannnan umurnin na kotu yanzu komi zai tsaya.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Facebook page .katsina city News