Dan sanda ya ki karbar cin hanci na N160,000 a Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes30032026_175229_FB_IMG_1774893088891.jpg



Ana zargin matasa da safarar kwaya da kauranci

Wani jami’in dan sanda mai mukamin ASP, Kabiru Garba, ya ki karbar cin hancin naira 160,000 da wasu matasa da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi da kuma aikata kauranci suka yi yunkurin ba shi domin a sake su.

Majiyoyi sun shaida wa Katsina Times cewa matasan, wadanda dukkansu ke kasa da shekaru 25, sun hada da Almustapha Muhammad mai shekaru 23 da Ibrahim Abdullahi mai shekaru 22, duk daga unguwar Jan Bango a Katsina.

Rahotanni sun ce wani matashi mai suna Abdullahi daga Kofar Soro ne ya yi yunkurin ba jami’in kudin cin hancin domin a saki wadanda ake zargin.

Sai dai ASP Kabiru Garba ya ki amincewa da kudin, yana mai cewa dole ne ‘yan sanda su kammala bincike kafin daukar mataki. Ya kara da cewa idan aka tabbatar ba su da laifi za a sake su, amma idan aka same su da laifi za a gurfanar da su a gaban kotu domin hukunci.

An ruwaito cewa an kama matasan ne dauke da wani kunshi da ake zargin tabar wiwi ce, tare da zargin cewa suna da hannu a ayyukan kauranci da ke kara yaduwa a jihar.

Kokarin jin ta bakin jami’in dan sandan bai yi nasara ba, haka kuma ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ba, domin layin wayoyinsu ba su shiga.

Follow Us