Gidauniyar Dansadau Ta Raba Tallafin Sama da Naira Miliyan 30 Ga Jam’iyyar ADC a Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes08032026_002436_Screenshot_20260308-012316.jpg



Katsina Times

Gidauniyar Musa Sada Dansadau (Dan Sadau Foundation) ta raba tallafin kuɗi sama da naira miliyan 30 domin tallafawa ayyukan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Katsina.

Da yake bayyana hakan a hedikwatar jam’iyyar ADC ta jihar, Musa Sada Dansadau ya ce suna shirye su ci gaba da tallafa wa jam’iyyar ta kowace fuska domin ganin ta samu ci gaba.

Ya bayyana cewa tallafin na daga cikin manufofinsa na taimakawa al’umma da kuma ƙarfafa jam’iyyar domin ta bunƙasa a faɗin jihar.

A cewarsa, za a bai wa ƙananan hukumomi 11 da ke cikin mazabar Katsina Central Senatorial District tallafin kuɗi na naira miliyan 11 domin ƙarfafa ayyukan jam’iyyar a matakin ƙasa.

Haka kuma, ya ce an ware naira miliyan 10 ga kwamitin da ke kula da rajistar mambobin jam’iyyar ADC domin tallafa musu wajen gudanar da ayyukansu.

Sauran mambobin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki kuwa za a raba musu aƙalla naira miliyan 10 a matsayin tallafi domin ƙarfafa gwiwarsu a harkokin jam’iyyar.

A ƙarshe, Dansadau ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar da su ji tsoron Allah wajen gudanar da ayyukansu, tare da ba kowa dama cikin adalci, musamman ga waɗanda ke son ba da gudummawa ko kuma su tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar.

Ya kuma bayyana cewa a shirye yake ya tsaya takara a cikin jam’iyyar ba tare da wani fargaba ba.

A nasa jawabin godiya, Shugaban jam’iyyar ADC na Jihar Katsina, Musa Wamba, wanda Salisu Uli ya wakilta, ya nuna jin daɗinsa kan tallafin da aka bayar.

Ya tabbatar da cewa shugabancin jam’iyyar zai yi adalci ga dukkan ‘yan takara da kuma mambobin jam’iyyar baki ɗaya.

Follow Us