Duwan Ya Jinjinawa Gwamna Radda Kan Nasarar Zaɓen Sabbin Shugabannin APC a Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes05032026_123940_FB_IMG_1772714127121.jpg


Mai bai wa Gwamnan Jihar Katsina shawara kan harkokin jam’iyyu, Alhaji Shafi’u Duwan, ya bayyana jinjinarsa da godiyarsa ga Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, bisa yadda aka gudanar da zaɓen sabbin shugabannin jam’iyyar APC na jihar daga matakin unguwanni har zuwa matakin jiha cikin nasara.

A cikin wata takardar sanarwa da ya fitar, Alhaji Shafi’u Duwan ya bayyana cewa an gudanar da zaɓukan cikin natsuwa, tsari da kuma hangen nesa, lamarin da ya sanya jihar Katsina ta zama abin koyi ga sauran jihohin ƙasar nan wajen gudanar da harkokin jam’iyya cikin lumana da tsari.

Ya ce nasarar da aka samu a zaɓen ta samo asali ne daga kyakkyawan jagoranci da kuma salon shugabanci na gaskiya da adalci da Gwamna Dikko Umaru Radda ke nunawa, wanda ya ba da damar gudanar da dukkan matakan zaɓen cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna.

Duwan ya ƙara da cewa sabbin shugabannin da aka zaɓa daga matakin unguwanni zuwa na jiha mutane ne da ke da kishin jihar Katsina da kuma ci gaban jam’iyyar APC, inda ya nuna kyakkyawan fata cewa za su yi aiki tukuru domin ƙarfafa jam’iyyar tare da tallafa wa manufofin gwamnatin jihar.

A cewarsa, sabbin shugabannin za su taimaka wajen ci gaba da aiwatar da tsarin gwamnatin Gwamna Radda na “gina yau domin kyakkyawar gobe”, wanda ke da nufin samar da cigaba mai ɗorewa ga al’ummar jihar Katsina.

Har ila yau, Alhaji Shafi’u Duwan ya bayyana cewa babbar nasarar da aka samu a zaɓen ita ce zaɓen sabon shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Bishir Gambo Saulawa, wanda ya ce mutum ne mai gogewa a fagen siyasa kuma wanda ya taso a manyan gidajen siyasa.

Ya ce Saulawa mutum ne da ya san yadda ake tafiyar da harkokin siyasa, ya fahimci dabarun gudanar da zaɓe da kuma yadda ake tafiyar da gwamnati, wanda hakan zai taimaka matuƙa wajen ciyar da jam’iyyar APC gaba a jihar.

Duwan ya ƙara da cewa suna da cikakken kwarin gwiwa cewa sabon shugaban jam’iyyar zai yi aiki kafada da kafada da gwamnatin jihar domin tabbatar da manufar Gwamna Radda ta gina sabuwar Katsina mai ɗorewa.

A ƙarshe, ya tabbatar da cewa shi da sauran magoya bayan jam’iyyar APC za su ba sabon shugaban jam’iyyar cikakken goyon baya domin ya samu nasarar sauke nauyin da aka ɗora masa, tare da nuna cewa ba kawai ‘yan jam’iyyar APC ba, har ma da sauran al’ummar jihar Katsina za su ba shi hadin kai saboda gogewarsa da kuma irin gudunmawar da ya bayar a muƙamai daban-daban da ya riƙe a gwamnatin jihar.

Follow Us