Kungiyar Dikko Project Movement ta sanar da amincewarta tare da bayyana cikakken goyon bayanta ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da kuma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Kungiyar ta bayyana wannan matsaya ne a wata sanarwa da shugabanta, Hon. Musa Yusuf Gafai, ya fitar a ranar Asabar, inda ya jaddada cewa goyon bayan ya samo asali ne daga abin da ya kira shugabanci nagari da manufofin ci gaba da shugabannin ke aiwatarwa a matakin ƙasa da jiha.
A cewar sanarwar, Dikko Project Movement za ta shiga sahun gaba tare da dukkan rassanta da mambobinta domin haɗa kai da sauran ƙungiyoyi masu kishin ci gaba, da nufin tabbatar da cewa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu nasara a kowane mataki na zaɓe mai zuwa.
Kungiyar ta kuma bayyana ƙudurin ta na wayar da kan jama’a da ƙarfafa haɗin kai tsakanin magoya bayan jam’iyyar domin cimma nasarar zaɓe cikin lumana da bin doka da oda.
Sanarwar ta ƙare da kira ga al’umma da su ci gaba da mara wa shugabanni baya domin dorewar zaman lafiya, cigaba da kwanciyar hankali a Jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya.