’Yan Najeriya Sama da 408,000 Ne Ke Gudun Hijira a Nijar, Kamaru da Chadi — Majalisar Ɗinkin Duniya

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes09012026_090316_FB_IMG_1767948925730.jpg

’Yan Najeriya Sama da 408,000 Ne Ke Gudun Hijira a Nijar, Kamaru da Chadi — Majalisar Ɗinkin Duniya

By Katsina Times

Abuja — Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa ’yan Najeriya sama da 408,000 ne ke ci gaba da rayuwa a matsayin ’yan gudun hijira a ƙasashen Jamhuriyar Nijar, Kamaru da Chadi, sakamakon matsalolin tsaro da suka addabi yankin Arewa maso Gabashin ƙasar.

Wannan bayani na kunshe ne a cikin rahoton Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR), wanda ya danganta yawan gudun hijirar da rikicin Boko Haram da ISWAP, wanda ya jawo kashe-kashen jama’a, lalata gidaje, da durƙusar da rayuwar al’umma a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.

Rahoton ya nuna cewa Jamhuriyar Nijar ce ke dauke da mafi yawan ’yan gudun hijirar Najeriya, yayin da Kamaru ke matsayi na biyu, sai kuma Chadi ke biye da su wajen karɓar ’yan Najeriya da suka tsere daga rikicin.

UNHCR ta bayyana cewa duk da kokarin da ake yi na mayar da ’yan gudun hijira gida, har yanzu mutane da dama na jin tsoron komawa saboda rashin tabbataccen tsaro a yankunansu na asali.

Hukumar ta kuma yi kira ga gwamnatocin kasashen yankin da ƙungiyoyin agaji da su ƙara zuba jari wajen tallafa wa ’yan gudun hijira, tare da samar da hanyoyin dawo da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta jaddada cewa magance matsalar tsaro da samar da ayyukan raya kasa su ne muhimman hanyoyin da za su rage yawan gudun hijira da kuma tabbatar da dawowar jama’a gidajensu cikin kwanciyar hankali.

Follow Us