Ma’aikatan Jami’ar UMYU Sun Fara Yajin Aikin Gargadi Na Mako Biyu

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes04112025_182826_FB_IMG_1762181451713.jpg


Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times 

Ƙungiyoyin ma’aikata a Jami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU) ta Katsina sun fara yajin aikin gargadi na mako biyu saboda gazawar Gwamnatin Jihar Katsina wajen cika yarjejeniyoyin da aka kulla tun shekara ta 2020 dangane da jin daɗin ma’aikata da kuma ikon gudanar da jami’ar cikin ‘yanci.

Dr. Murtala Isah Kwara ne bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a harabar Sakateriyar ƙungiyar ASUU da ke jami’ar ranar talata 4 ga Nuwamba 2025, inda shugabannin ƙungiyoyin suka hadu akan cewa yajin aikin ya zama dole saboda halin ko-in-kula da rashin ɗaukar alhakin da Gwamnatin Jihar ta nuna.

Ƙungiyoyin da suka shiga yajin aikin sun haɗa da ASUU, SSANU, NAAT da NASU, waɗanda dukansu suka yi magana da murya ɗaya kan bukatun da har yanzu ba a biya su ba.

A cewar shugabannin ƙungiyoyin, matsalolin da ba a warware ba sun haɗa da aiwatar da tsarin albashi da ya dace ga ma’aikatan jami’a, matsalar kwace ikon gudanar da shafin yanar gizon jami’ar — wanda hakan ya shafi rajista, jarrabawa, da bayanan karatu — da kuma ƙarin kuɗin makaranta ba tare da shawarar da ta dace ba.

Sun kuma nuna rashin jin daɗinsu kan tilasta amfani da Treasury Single Account (TSA) wanda yake sabawa dokar gudanar da jami’o’i da ta tanadi cewa kowace jami’a tana da cikakken ikon gudanarwa.
Haka kuma sun koka da tsarin fansho da Gwamnati ta aiwatar ba tare da tattaunawa da ma’aikata da abin ya shafa ba, lamarin da suka ce ya saba wa tsarin Gwamnatin Tarayya.

“Babu ɗaya daga cikin yarjejeniyoyin da muka cimma da Gwamnatin Jihar da aka aiwatar har yanzu, duk da haƙuri da jinkirin da muka nuna tun shekara ta 2020,” in ji shugabannin ƙungiyoyin.
“Mun ba da ƙarin makonni uku domin ta cika alkawuranta, amma babu wani abin a zo a gani.”

Ƙungiyoyin sun jaddada cewa wannan mataki ba na gaggawa ko wasa ba ne, illa dai mataki na ƙarshe bayan duk hanyoyin tattaunawa sun gaza.

“Yakinmu ba domin son kai ba ne, sai domin ingancin ilimi da makomar ‘ya’yanmu,” in ji ƙungiyoyin, suna neman fahimta da goyon bayan ɗalibai, iyaye, da al’ummar Katsina gaba ɗaya.

Duk da haka, ƙungiyoyin sun bayyana cewa sun samu ci gaba wajen tattaunawa da hukumar inshorar lafiya ta jihar, KACHIMA, inda hukumar ta amince da ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar kuma ta nuna shirinta na yin gyare-gyare.

Sun yi gargadin cewa idan har ba a samu wani ci gaba ba bayan wannan yajin aikin gargadi na mako biyu, za su sake taro domin yanke shawarar matakin gaba.

Follow Us