Katsina Ta Kammala Horas da Ma’aikatan Lafiya Kan Ingantacciyar Ciyarwa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes11072025_180059_FB_IMG_1752256776458.jpg

Muhammad Ali Hafizy | Katsina Times

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Katsina ta kammala wani muhimmin taron horaswa na kwanaki huɗu kan tsarin Ingantacciyar Ciyarwa, wanda a Turance ake kira Integrated Management of Acute Malnutrition (IMAM), a ranar Juma’a, 11 ga Yuli, 2025. A dakin taro na Alhujrat dake Katsina 

Taron horon ya gudana ne tare da haɗin gwiwar Bankin Duniya (World Bank) babbar cibiyar ba da tallafi ga kasashe don ci gaba da kuma ƙungiyar Accelerating Nutrition Results in Nigeria (ANRiN), wato Shirin Hanzarta Samun Ingantaccen Ciyarwa a Najeriya.

Wannan aiki yana karkashin sabon tsarin tallafin lafiya na Sector Wide Approach (SWAp), wanda ke nufin haɗin gwiwar dukkanin masu ruwa da tsaki a fannin lafiya domin tabbatar da daidaito da inganci a aiwatar da shirye-shirye a fadin jihar.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Katsina, Hon. Musa Adamu Funtua, ya bayyana godiyarsa ga Bankin Duniya (World Bank) da kuma ANRiN bisa irin goyon bayan da suka bayar wajen gudanar da wannan horo, yana mai cewa hakan wani gagarumin ci gaba ne ga jihar Katsina.

“Tabbas wannan horo zai taimaka matuƙa wajen dakile yawaitar cututtuka da yara kanana ke fuskanta sakamakon rashin samun abinci mai gina jiki,” in ji shi.

Ya ce horon ya zo a daidai lokacin da gwamnatin Jihar Katsina karkashin Gwamna Malam Dikko Umar Radda ke ƙoƙarin magance matsalolin da suka shafi ƙarancin abinci da ciyarwa. Ya bayyana cewa gwamnatin ta raba ingantattun iri, takin zamani da kuma kayan aikin noma ga dukkan kananan hukumomi 34 a karkashin Katsina State Agricultural and Rural Development Authority (KATARDA), wato Hukumar Raya Noma da Karkara ta Jihar Katsina, tare da horar da manoma don ƙara samar da abinci mai gina jiki.

A ƙarshe, Kwamishinan ya yi kira ga al’umma, kungiyoyi, shugabanni da sauran masu ruwa da tsaki da su bayar da gudummawarsu ta hanyar goyon bayan shirye-shiryen samar da abinci mai inganci domin tabbatar da ingantacciyar lafiya ga jama’ar jihar Katsina.

Follow Us