Jirgin Karshe Na Majihatan Jihar Katsina Karkashin Jagorancin Amirun Hajji Na Jihar Ya Dawo Gida.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes02072025_152524_IMG-20250702-WA0027.jpg

‎Daga Muhammad Ali el Hafizy 
@ Katsina tmes



‎A misalin ƙarfe goma saura kwata na ranar Laraba 02 ga watan Yuli na shekarar 2025, jirgin ƙarshe na Majihatan jihar Katsina ya sabka a filin sauka da tashin jirage na Malam Umaru Musa Yar'adua dake cikin garin Katsina.
‎Jirgin ya dawo ne karkashin jagorancin Amirul Hajji na jihar kuma mataimakin gwamnan jihar Alhaji Faruq Lawal Jobe, wanda ya samu rakiyar sauran majihatan da suka dawo tare.
‎Ahaji Faruq Lawal Jobe ya shaida ma manema labarai cewa "Mun samu damar gabatar da aikin hajji tare da sauran alhazan jihar Katsina lafiya ba tare da samun wata matsala ba" inji shi.
‎Ya kara da cewa "Alhazan jihar Katsina sun yi bakin kokarin su wajen ganin cewa sun kiyaye duka dokokin da aka sanya domin ganin an gudanar da ibadar hajji ta wannan shekarar lafiya" inji shi.
‎Daga karshe ya yi godiya ga gwamna Malam Dikko Umar Radda bisa ga kokarin da yayi na tallafa ma alhazzan da yayi, da kuma irin gudunmawar da gwamnati ta bada, tare da sauran kwamitocin da suka taimaka wajen gabatar da ibadar lafiya.

Follow Us