Daga Garba Abu Abdullahi Jikamshi
Rahotanni daga yankin Arewa Maso Gabas sun bayyana cewa Mayakan Boko Haram sun shirya kwanton bauna ga jerin gwanon motocin Dantakarar Gwamnan jihar Borno na Jam'iyyar APC, Injiniya Mustafa Gubio.
Kamar yadda bayanai su ka tabbatar, lamarin ya faru ne a daidai lokacin da Dantakarar ke Kan hanyar sa ta dawowa Maiduguri, bayan wata ziyarar godiya da ya kai ga al'ummar Damasak.
Mayakan na Boko Haram sun dasa nakiya ne a kan babbar hanyar da ta hada Gubio da Kareto da Damasak, Wanda Kuma a ka yi rashin sa'a wata motar Jami'an Tsaro ta taka.
Bayan samun fashe-fashen nakiyoyin ne Mayakan su ka yi yunkurin dirar ma jerin gwanon motocin.
To sai dai kuma Mayakan na Boko Haram sun fuskanci turjiya daga gamayyar Jami'an Tsaro da su ka hada da sojoji da Yansanda da Jami'an JCF, in da a ka sha artabu da barin wuta.
Harin dai ya kara fito da dimbin kalubalen tsaro da ke damun yankin na Arewa Maso Gabas.


Comments (0)
No comments yet. Be the first to share your thoughts!