An Karyata Zargin Bai wa Ma’aikaci Mukamin Ma’aji Ba Bisa Cancanta Ba a Musawa

Daga Hadi Abdullahi@ Katsina TimesWasu ma’aikatan Karamar Hukumar Musawa sun karyata zargin da aka yi a baya cewa an bai wa wani ma’aikaci mukamin Ma’aji alhali bai cika sharuddan cancantar…

Katsina City News September 02, 2026  ·  12:00 AM
| 32 Views
An Karyata Zargin Bai wa Ma’aikaci Mukamin Ma’aji Ba Bisa Cancanta Ba a Musawa
An Karyata Zargin Bai wa Ma’aikaci Mukamin Ma’aji Ba Bisa Cancanta Ba a Musawa


Daga Hadi Abdullahi

@ Katsina Times

Wasu ma’aikatan Karamar Hukumar Musawa sun karyata zargin da aka yi a baya cewa an bai wa wani ma’aikaci mukamin Ma’aji alhali bai cika sharuddan cancantar rike mukamin ba.

Ma’aikatan, wadanda suka yi bayani kan batun, sun bayyana cewa ma’aikacin da aka bai wa mukamin, Bello Usman, yana da takardar Diploma a fannin harkokin kuɗi, tare da Digiri, kuma ya shafe shekaru masu yawa yana aiki a bangarori daban-daban da suka shafi harkokin kuɗi da asusun gwamnati.

Sun kara da cewa, ya kai mataki na 15 a aikin gwamnati, wanda a cewarsu ya kara tabbatar da gogewarsa da cancantarsa wajen rike wannan mukami.

Masu kare nadin nasa sun ce an yi la’akari da dukkan sharudda da ka’idojin aikin kananan hukumomi kafin a ba shi mukamin, suna jaddada cewa ya cika ka’idojin da suka dace da nadin.

Sun kuma bayyana cewa, saboda kwarewarsa da cancantarsa, an taba tura shi daga wata karamar hukuma zuwa wata domin gudanar da ayyukan da suka shafi harkokin kuɗi.

A cewarsu, abin da ya kamata a yi tambaya a kai shi ne, idan da gaske akwai korafi kan cancantarsa, me ya sa irin wannan korafi bai taso daga wuraren da ya taba aiki a baya ba, sai yanzu a Karamar Hukumar Musawa?

Ma’aikatan sun ce batun ya samo asali ne daga rashin jituwar wasu masu neman mukamin, inda wasu suka samu damar rike mukaman, wasu kuma ba su samu ba.

A cewarsu, wanda bai samu mukamin ba ne zai iya nuna rashin jin daɗi tare da gabatar da korafi, amma hakan ba yana nufin cewa wanda aka bai wa mukamin bai cancanta ba.

Advertisement

NRS Gateway

Tarihin Aikin Bello Usman

Bello Usman ya fara aikin gwamnati ne a ranar 1 ga Satumba, 1996.

A shekarar 1997, ya fara aiki a matsayin Akawu a Karamar Hukumar Musawa, inda ya ci gaba da aiki har zuwa shekarar 1999.

Daga bisani, ya ci gaba da gudanar da ayyuka daban-daban a bangarorin harkokin kuɗi da asusun gwamnati. A shekarar 2003, ya yi aiki a matsayin Akawu a Sashen Aikin Gona na karamar hukuma.

A shekarar 2005, ya zama Akawu a Sashen Ilimi da Fadakarwa na karamar hukuma.

Daga baya kuma, ya zama cikakken Akanta a Sashen Aikin Gona na Karamar Hukumar Matazu a shekarar 2018.

Ya kuma yi aiki a matsayin Akanta a Sashen Ayyuka na Karamar Hukumar Kusada, kafin daga bisani ya koma irin wannan matsayi a Sashen Ayyuka na Karamar Hukumar Malumfashi a shekarar 2021.

A shekarar 2025, ya sake komawa aiki a matsayin Akanta a Sashen Ayyuka na Karamar Hukumar Kusada.

Daga wannan matsayi ne aka daga shi zuwa mukamin Ma’aji, bisa la’akari da tarihinsa na aiki, gogewarsa da kuma cancantar da masu goyon bayan nadin nasa suka ce ya mallaka.

Masu bayyana ra’ayinsu kan batun sun bukaci jama’a da su yi nazari mai zurfi kan tarihin aikin Bello Usman da kwarewar da ya samu tsawon shekaru, kafin yanke hukunci kan zargin da ake yi dangane da cancantarsa wajen rike mukamin Ma’aji.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 5 + 5?