ZIYARATA KASUWAR CINIKIN BAYIN GABASHIN AFIRIKA
- Katsina City News
- 03 Oct, 2023
- 782
Cikin wuraren tarihi da na ziyarta a tsibirin Zanzibar,shi ne: Tsohuwar Kasuwar cinikin bayi.
Lokacin da muka isa,farko sai da wata jami'ar tsaro ta tantance mu,daga nan, muka wuce wurin da ake saida tikitin shiga. A matsayina na wanda ba dan kasa ba,sai da na biya shiilin kudin Tanzania dubu sha daya da dari biyar kafin a barni in shiga. Ka ga yadda Zanzibar ke sayar da mummunan tarihinta na cinikin bayi.
Amma a gaskiya ban yi asarar kudina da lokaci ba.Domin idan kana son sanin yadda cinikin bayi a gabashin Afirika ya gudana to da ka zo wannan wurin za ka samu bayanan da kake so.
Bayan mun shiga,na fara arba da wasu mutum-mutumi na bayi guda biyar,uku daga cikinsu an daure su da sarka a wuya. Dukkan su, suna cikin wani rami ne.
Wannan yana nuna bakin tarihin cinikin bayi a Zanzibar,wadda ta kasace cibiyar hada-hadar bayi a karni na Sha tara .
Lokacin da larabawan daular Omani suka kori turawan Portugal daga Zanzibar,Sultan Sayyid Sa'id ya habbaka noman karamfani . Zanzibar ta kasance cibiyar noman karamfani a duniya. Noman karamfani na bukatar ma'aikata,wannan bukata ce ta rura wutar cinikin bayi,wanda ake samo su ta hanyoyi daban-daban, cikin harda ta yaki,kame,ko a sawo a arha.
Bukatar hauren giwa tsakanin turawa ,shima ya kara rura wutar cinikin bayi a yankin ,saboda bayin ne ke dakon hauren giwar zuwa gabar teku,inda daga nan ake wucewa da su kasashen turai da Amurka.
Ana sarrafa hauren giwa wurin yin kayan kida na fiyano, kayan ado da sauran kayan kyale-kyale.
Wannan wurin tarihi na kumshe da cikakkun bayanai game da yadda aka gudanar da safarar bayi a yankin tekun Indiya.
Tarihin Muguntar mutum akan dan uwansa mutum, da na gani karara a wannan cibiya,ya tuna man maganar da Shakespeare yai cewa: akan saurin manta alheri fiye da mugunta.