Tarihin Unguwar Filin Bugu, a cikin Birnin Katsina
- Katsina City News
- 26 Sep, 2023
- 1046
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Filin Bugu tana bisa babbar hanyar da ta tashi daga Chake zuwa Sagi.
Daga bangaren gabas unguwar ta yí iyaka da Gambarawa, ta sashen yamma ta yi iyaka da Sararin Tsako, daga arewa ta yi iyaka da Farin Yaro kuma daga kudu ta yi iyaka da Sagi.
Ita wannan unguwa ta Filin Bugu asalinta 6angare ne na unguwar Chake da Gambarawa. Unguwar ta samo sunanta ne daga bugun gidaje da en'e din Katsina ta yí a wurin
shekarar 1965, a zamanin Sarkin Katsina Usman Nagogo Makasudin wannan aikin da en'e ta yi shi ne domin a samar da titin mota daga Chake zuwa Sagi don saukaka zurga-zurga da kyautata rayuwar mazauna wurin. Bayan an kamala aikin.
Sai mutane suka sanya ma wurin suna "filin bugu' watau filin da a ka yi bugun gidaje. Bayan an samar da titin mota, unguwar ta ci gaba da bunkasa. Wannan cigaba ya samu ne sabili da kafuwar kasuwar "Hi-Mata" a farkon 1980.
It Hi-Mata an ce wata mace ce wadda gidanta ke a nan filin bugu. Bayanai sun nuna cewa tana sana'ar sayar da rogo da ganyen kwado da kulikuli da sauransu, a nan gefen hanya. A hankali sai wurin ya habaka, har ya zama 'yar karamar kasuwa. Kasuwar Hi-Mata ta zama cikakkiyar kasuwa a cikin shekarar 1998.
Wannan ya faru ne saboda tayar da tsohuwar
kasuwar Katsina zuwa sabuwar Kasuwa ta zamanı da Gwamnati Jihar Katsina ta gina a hanyar Dutsin-ma. Dalilin haka wasu daga cikin yan kasuwa suka mayar da harkokin kasuwancinsu zuwa Hi-Mata domin rashin samun runfuna da nisa da sabuwar kasuwa ta yi da cikin gari a v wancan lokacin. Amma duk da wannan cigaba, kasuwar Hi-Mata ta kasance a yanayin kasuwar karkara domin ba ta ci da runfuna na dindindin, da isasshen fili.
Kauyukan da ke gewaye da Birnin Katsina kamar Bugaje, Daga, Dutsen Safe, Ɗaddara suna kawo amfanin gona da Dabbobi ko wace ranar Talata da Juma'a ranar da Kasuwar ke ci.
Mun ciro wannan Tarihi daga Littafin Tarihin Unguwannin Birnin Katsina da kewaye wanda "Hukumar Binciken Tarihi da kyautata Al'adu ta jihar Katsina ta Buga.