TSOFAFFIN ƘANANAN HUKUMOMI DA MUKE DASU GUDA BAKWAI A FAƊIN JIHAR KATSINA.
- Katsina City News
- 05 Dec, 2024
- 116
WANDA AKA KIRKIRA BAYAN SAMUN JIHA A 23rd-September-1987.
1. Katsina
2. Daura
3. Funtua
4. Dutsinma
5. Kankia
6. Malumfashi
7. Mani
An yi wadannan ƙananan Hukumomi lokacin mulkin soja na Col. Abdullahi Sarki Mukhtar 1987-1988
Tun daga wannan lokaci, ba'a sake yin wasu wasu ƙananan Hukumomi ba sai lokacin Col. Lawrence A. Onoja, Wanda ya karɓi ragamar mulki daga 1988-1990.
A cikin wa'adin mulkin sa ne aka ƙara ƙirƙiro wasu sabbin ƙananan Hukumomi guda Bakwai suka zama 14 kamar haka.
A Ranar 15th-May-1989.
1. Safana
2. Faskari
3. Kaita
4. Ƙanƙara
5. Mashi
6. Musawa
7. Zango
Bayan Col. Lawrence A Onoja ya gama wa'adin mulkin sa, sai Col. Yahaya John Madaki ya karɓi ragamar mulki/shugabancin jihar Katsina, a cikin shekara ta 1990-1992.
Inda Col. John Y. Madaki, ya ƙara ƙirƙirar wasu sabbin ƙananan Hukumomi guda 12 a jihar Katsina, a cikin shekara ta 1991.
A Ranar 21st-September 1991.
1. Rimi
2. Matazu
3. Mai'aduwa
4. Kurfi
5. Kafur
6. Jibia
7. Ingawa
8. Ɗanja
9. Bindawa
10. Batsari
11. Batagarawa
12. Bakori
Tun daga wannan lokacin ne, jihar Katsina ta ke da ƙananan Hukumomi guda 26.
Daga wannan lokacin ne, sai aka faɗa cikin mulkin Siyasa na farar Hulla, inda manyan jam'iyyun adawa irin su SDP da NRC suka fa fa ta, daga ƙarshe jam'iyar NRC ta yi nasara lashe zaɓen, wanda Tsohon Gwabnan farar Hulla Alhaji Sa'idu Barda ya ɗare bisa kujerar Gwamnan Katsina daga 1992-1993.
*Har mutane na cewa, angulu da kan zabo" wai ma'ana shugaban ƙasa na soja gwabnoni na Farar Hula.*
Bayan wa'adin mulkin sa ya ƙare, sai sojojin suka ƙara amsar ragamar mulkin jihar Katsina, inda aka turo Navy Captain Emanuel A. Acholonu ya yi mulki daga 1993-1996.
Daga gare shi ne kuma, aka canza ya zuwa Col. S.B Chama, Wanda ya yi Gwabna daga 1996-1998.
Col. Sama'ila Bature Chama, shine wanda ya ƙara yawan ƙananan Hukumomi guda 8 suka zama 34, wanda muke da su har ila yau.
A Ranar 17th-December-1996
1. Ɓaure
2. Ɗandume
3. Dutsi
4. Sabuwa
5. Charanci
6. Ɗanmusa
7. Kusada
8. Sandamu.
Jihar Katsina ta yi Gwabnoni na sojoji guda Shida 6, na farar Hula ya zuwa yanzu muna da guda Biyar.
1. Col. Abdullahi Sarki Mukhtar 24th- Sep, 1987-1988
2. Col. Lawrence A Onoja 1988-1990
3. Col. John Y. Madaki 1990-1992
4. Alh Sa'idu Barda 1992-1993
5. Navy Captain Emanuel A Acholonu 1993-1996
6. Col. S.B Chama 1996-1998
7. Lt Col. J Akaagerger 1998-1999.
Daga gare shi mulkin soji ya kau aka dasa na farar Hula wanda muke cikin sa a yau.
Inda aka zaɓi jam'iyar PDP ƙarƙashin Gwabna Malam Umaru Musa Yar'adua a shekara ta 1999-2003.
Sannan a karo na biyu jam'iyar ta ƙara yin nasarar lashe zaɓe a shekara ta 2003-2007.
8. Gwamna Malam Umaru Musa Yar'adua 1999-2003
2003-2007.
Bayan wa'adin mulkin sa ya ƙare, sai jam'iyar ta ƙara tsaida sabon ɗan takarar ta Barrister Ibrahim Shema.
9. Barrister Ibrahim Shehu Shema 2007-2011
2011-2015.
Bayan wa'adin mulkin sa ya ƙare, sai aka samu sauyin shugabanci na jam'iya, inda jam'iyar adawa ta APC ta yi nasarar lashe zaɓe a shekara ta 2015.
10. Rt.Hon. Aminu Bello Masari 2015-2019
2019-2023
Bayan wa'adin mulkin sa ya kare, jam'iyar ta sake tsaida ɗan takarar ta a karo na Uku inda kuma ta yi nasarar lashe wannan zaɓe a shekara ta 2023 zuwa yau.
11. Malam Umar Dikko Raɗɗa Shine Gwabnan jihar Katsina 2023-
A JIHAR KATSINA NE WASU DAGA CIKIN YA'YAN TA, A MATAKIN AIKIN JAMI'AN TSARON KASAR NAN NA FANNONI DABAN DABAN SUKA YI ZARRA.
1. General Muhammadu Buhari, GCFR: President of the Federal Republic of Nig
2. General Shehu Musa Yar'adua, GCON: Vice president of the Federal Republic of Nig (Tafidan Katsina)
3. General Hassan Usman Katsina OFR: Governor of northern State (Ciroman Katsina)
4. General Ahmadu Daku: Governor of the military Government Kano/Sokoto State
5. Col. Abdulmuminu Aminu: Governor of the military Government of Borno State
6. Col. Umar Faruk Ahmadu Ɗan baiwa: Governor of the military Government Cross River/Kaduna State
7. Col. Iliyasu Wali, OON: Chief Imam of the Nigerian Armed forces (Walin Katsina)
8. General Amadi Rimi, OON: Nigerian Army Medical Corp's (Baraden Katsina)
9. Major General Abba Abdulƙadir: Chairman of Nigerian Security Printing and Minting Company
10. Brigadier General Maharazu Tsiga: The Director General NYSC
11. Inspector General of Police: Muhammad Dikko Yusuf.
12. Inspector General of Police: Ibrahim Ahmadu Kumasi, GCON (Sardaunan Katsina)
13. Amb. Muhammad Lawal Rafindadi: Director General of the Nigerian Security Organization
14. Amb. Zakari Ibrahim, CON. Director General, National Intelligence Agency (Talban Katsina)
15. Amb. Ahmed Rufa'i, CFR: Director General, National Intelligence Agency (Sardaunan Katsina)
16. Dikko Abdullahi Inde, MFR: Comtroller General of Nigerian Customs Services
Wajen da muka yi kurakurai ko tuntuɓen alƙalami ayi mana afuwa, inda kuma ke da wani ƙarin bayani muna maraba da shi.
Rubutawa: Zaharaddeen Ibrahim Katsina (Mayanan Safana)