KIWON LAFIYA: CUTAR RASHIN AIKIN SASHEN JIKI (PARALYSIS)
- Katsina City News
- 24 Nov, 2024
- 66
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
Wannan ciwo na rashin aiki a wasu sassan jiki yana faruwa ne sakamakon matsaloli da suka shafi jijiyoyin zuciya, kwada, ko kuma kafofin da jini ke gudana.
24.1 ABUBUWAN DA KE KAWO SHI
1. Fashewar wata kafar jini da ke cikin kwalwa, wanda ke haifar da zubar jini a cikin kwalwar.
2. Rauni ko cuta da kan shafi kwalwa.
3. Yawan shan kwayoyin magani barkatai.
4. Wanzuwar gundurin jini a jijiyojin da ke ba wani bangare jini a cikin kwalwa.
5. Ciwo ko rauni da kan shafi lakka.
6. Wanzuwar iska a cikin jijiyojin da ke ba wani sashen kwalwa jini (cerebral embolism).
24.2 YADDA CUTAR KE FARUWA
A dalilin matsanancin hawan jinni, daya daga cikin jijiyojin da ke ba wani sashe na kwalwa jini zai fashe, wanda zai haifar da zubar jini a cikin kwalwa da kuma rashin aiki a wasu jijiyojin da ke cikin kwalwar. Sakamakon haka, mutum zai kasa sanin inda kansa yake. Wannan zai iya jawo rashin aiki a sashen jiki na hagu ko dama, wanda ke nuni da cutar.
- Idan a sashen hagu na kwalwa ne abin ya faru, mutum zai gaza yin amfani da sashen jikinsa na dama kuma zai rasa iya magana. Wannan saboda na'urar da ke sa mutum ya yi magana tana zaune a bangaren hagu na kwalwar.
- Idan kuma a sashen dama ne abin ya faru, mutum zai rasa sashen jikinsa na hagu amma zai iya magana.
- A wasu lokuta, mutum zai rasa damar amfani da dukkan jikinsa, musamman idan matsalar ta shafi lakar da ke wajen kasussan wuya (cervical vertebrae). A wasu lokuta, mutum na iya rasa amfani da rabin jikinsa daga kugu zuwa kasa.
24.3 ALAMOMIN WANNAN CIWO
Alamomin wannan ciwo suna da nau'i uku:
1. Cerebral Hemorrhage (Taruwar Jini a Cikin Kwalwa): Wannan yana faruwa sakamakon tashin hankali kamar fada ko hadari. Wadanda suka samu wannan matsala, idan aka auna jininsu, za a ga ba su da hawan jini.
2. Cerebral Thrombosis (Iska a cikin Jiyoyin Kwalwa): Mutuwar sashen jiki na faruwa musamman idan mutum yana barci, kuma lokacin tashi zai fuskanci rashin iya magana, rasa sanin inda kansa yake, ko kuma rashin iya motsa wani bangare na jikinsa. Wannan ciwon na iya kasu kashi biyu:
- Matsananci: Mutum na iya farfadowa ko kuma ya wuce ba zai farfado ba.
- Mild (Mai Sauƙi): Mutum na iya warkewa cikin 'yan mintoci ko kwanaki biyu.
24.4 YADDA ZA A KULA DA MARAR LAFIYA
Yawancin masu fama da wannan matsala ana kwantar da su a asibiti domin kula da lafiyarsu. A asibiti, ana amfani da na'urorin kulawa kamar su:
- Kulawa da numfashi: Ana kwantar da marar lafiya ko a sashen hagu ko dama ko kuma a rigingine. Idan akwai matsalar numfashi, ana sanya masa na'ura mai taimakawa wajen shakar iska.
- Kulawa da idanu: Za a wanke idanuwa da ruwa mai tsafta sannan a shafa masu man basilin ko maganin da likita ya rubuta.
- Abinci: A farkon kwanakin, za a ba marar lafiya abinci ta hanyar robar na’ura (Nasogastric tube). Bayan farfadowa, za a fara ba shi abinci mai ruwa sannan a canza zuwa abinci na yau da kullum.
- Kulawa da baki da fitsari: Za a rinka wanke bakin marar lafiya da kuma sanya robar fitsari don kula da fitsari da aka saki ba tare da sani ba.
24.5 TAIMAKON MARAR LAFIYA
Bayan kwantar da marar lafiya a asibiti, za a koyar da shi yadda zai kula da kansa. Wannan yana taimakawa wajen motsa jiki da farfadowa. Misali, marar lafiya na iya koyon zama ba tare da an rike shi ba, ko tashi da kansa.
- Magunguna: Za a rubuta magungunan da suka dace da dalilin ciwon, kamar magungunan hawan jini idan hawan jini ya haifar da matsalar.
- Kulawa a gida: A lokacin sallama daga asibiti, za a ci gaba da kula da marar lafiya ta hanyar bashi shawara kan abinci da sauran magunguna.
Mun dauko daga Littafin "Kula Da Lafiya" Na Safiya Ya'u Yemal