KIWON LAFIYA: CUTAR HUKA (TIBI)
- Katsina City News
- 17 Nov, 2024
- 156
Cutar huka, wadda aka fi sani da tarin fuka (tibi), tana daga cikin manyan cututtukan da ke kawo barazana ga rayukan mutane. Wannan cuta mai tsanani ana daukar ta ta hanyar cutar TB, kuma ta fi kama huhu. Duk da haka, tana iya kama wasu sassan jiki, kamar kashi, lakka, da makamantansu.
YADDA CUTAR KE SHIGA JIKI:
1. Ta hanyar shakar iska: Idan aka shaki iska mai dauke da kwayar cutar.
2. Ta hanyar shan madarar shanu: Shan madarar shanu da ba a tafasa ba yana iya haddasa kamuwa da cutar.
3. Ta hanyar saduwa da masu cutar: Sumbatar mutum mai dauke da cutar, ko yara kanana shan nonon iyayensu mata da ke fama da cutar.
Cutar na iya zama cikin jikin mutum tsawon watanni hudu zuwa shekara daya kafin ta fara bayyana alamominta.
18.1 ALAMOMIN CUTAR HUKA (TIBI)
1. Tari mai tsanani, musamman da safe.
2. Tari mai dauke da majina ko jini.
3. Zazzabi mai sauki da rana, sannan zufa da dare.
4. Rashin nauyi (ramewa) tare da rashin sha’awar cin abinci.
5. Numfashi mai kara da wahala.
6. Ciwon kirji ko baya.
7. Taruwar ruwa a huhu.
8. A wasu lokuta, fata tana kara haske musamman a bakake.
Idan ba a kula ba, cutar kan kai ga:
- Rashin numfashi.
- Rashin sanin inda mutum yake (rashin hankali).
18.2 YADDA ZA A GANE CUTAR
1. Hoton kirji (X-ray) yana nuna huhu da cutar ta shafa.
2. Gwajin majina don gano kwayoyin cutar.
3. Tarihin shan taba yana iya taimakawa wajen gane cutar.
18.3 YADDA ZA A MAGANCE CUTAR TIBI
1. Shan magani: A rika shan maganin yadda likita ya tsara har tsawon watanni shida zuwa shekara. Kada a dakatar da shan maganin ba tare da izinin likita ba.
2. Hutu da kulawa: Mai fama da cutar ya huta sosai, kada ya yi wahalhalu.
3. Ciyarwa: A ci abinci mai gina jiki wanda ke kara karfin garkuwar jiki.
4. Tsabtace muhalli: Rufe baki lokacin tari ko atishawa, sannan kada a tofar da yawu a kasa.
18.4 CUTAR TIBI DA KASHI
Wannan nau’in cutar tana haddasa kumburi a kashi, wanda ke kawo radadi, gazawar amfani da sassan da abin ya shafa, da taruwar ruwa. Idan cutar ta tsananta, sassan da ke fama da ita za su kumbura, kuma a wasu lokuta za a ga ja a fata.
18.5 YADDA ZA A KIYAYE AUKUWAR CUTAR TIBI
1. Yin allurar rigakafi (BCG) ga yara.
2. Tabbatar da cewa duk wanda ke cikin gida yana da tsafta, musamman idan akwai mai cutar.
3. Shan madara da aka tafasa.
4. Gujewa shakar iska a inda mai cutar yake.
5. Tabbatar da cewa mai cutar ya kwana shi kadai tare da amfani da kayan cin abinci na kansa.
Da wannan bayani, yana da muhimmanci jama’a su yi hattara tare da bin matakan kariya don kauce wa kamuwa da wannan cuta mai hatsari.
Mun ciro daga Littafin Safiya Ya'u Yemal: Kula da lafiya