WASU DAGA CIKIN TSOFAFIN SARAUTU A MASARAUTAR KATSINA.
- Katsina City News
- 11 Nov, 2024
- 332
Mulki ko kuma shugabanci ko Sarauta a Katsina ya samo asaline daga Durbi Takusheyi ko kuma Durbawa, wanda daga Sarautar Durbi Takusheyi ne aka samu Sarautar Durbi, a Katsina, wada a halin yanzu itace tafi kowane Sarauta dadewa a Masarautar Katsina.
Daga cikin Sarautun da suka dade a Katsina akwai Sarautar Durbi da kuma Sarautar Danmasani.
SARAUTAR DURBI.
Kamar yadda aka nuna Kumayo jikan Bayajidda shine Sarki na farko daga cikin zuruar Durbawa wadanda suka shugabanci Durbi Takusheyi dake Kasar Mani ta yanzu. Wadannan Durbawa sun kwashe fiye da shekara dubu suna mulki a Durbi Takusheyi. Daga cikin Sarakunan Durbi Takusheyi akwai. 1. Kumayo. 2. Rumba Rumba. 3. Batare tare. 4. Korau. 5. Jin Narata. 6. Yanka tsari da kuma 7. Jibda Yaki Sanau. To daga wadannan Sarakunan ne aka samu asalin Sarautar Durbi a Katsina, a maimakon Durbi Takusheyi sai ta koma Durbin Katsina kuma Hakimin Mani. A lokacin da Muhammadu Korau ya zama Sarkin Katsina Musulmi na farko sai ya maida saraurar Durbi daga cikin manyan masu gari da suka hada da Durbi, da Yandaka da Gazobi da sauransu. Hakanan ma, lokacin da Mujaddadi Ummarun Dallaje ya zama Sarkin Katsina sai ya kara karfafa Sarautar Durbi inda ya dauko daya daga cikin manyan yayan shi, watau Saddiqu ya nada shi a matsayin Durbin Katsina, har dai ya zuwa yanzu yayan Sarki ne suke rike da wannan Saraura ta Durbi daga cikin zuruar Fulani Sullubawa. A maimakon Durbi Takusheyi sai ta koma Durbin Katsina kuma Hakimin Mani.
Sarautar Danmasani a Katsina.
Ita ma Sarautar Danmasani tsohuwar Sarauta ce wadda tun lokacin Sarakunan Habe aka farayin ta. Sarautar Danmasani ta samo asalintane daga wani Waliyi mai suna Abu Abdullahi ibn Gumehu ibn Masani Albarnawi Alkatsinawi, wanda aka fi sani da Danmasani. Shi dan masani asalin kakan nin shi mutanen Borno ne, sunzo Katsina tun lokacin Sarakunan Habe, shi kanshi Danmasani an haife shi a Katsina a shekarar 1595. Ya karankarance a littafafan addinin musulunci, yayi sharhi a kan littafin ishimawi, da kuma littafin Ishirinjya ta Alfa Zazi da sauransu. Yana bada shawara ga Sarakunan Habe na Katsina akan abinda ya shafi addinin musulunci. Danmasani ya rasu a shekarsr 1667, kuma har yanzu gidan shi da Masallacin shi, suna nan a Unguwar Masanawa dake cikin birnin Katsina. To tun daga wanna lokacinne, aka rika nada zuruar shi Sarautar Danmasani. Haka kuma daga gare shine Sarautar ta samo asali a Kasar Hausa, inda aka samu Danmasani Kano , Danmasani Sokoto da sauransu.
Wadannan sune dadaddun Sarautu a Masarautar Katsina, Sarautar Durbi ta faro tun Durbawa ita kuma ta Danmasani tun Habe.
Musa Gambo Kofar soro