MARIGAYIYA HAJIYA AMINA(GWAGGON KANO), MATAR SIR AHMADU BELLO GCON KBE SARDAUNAN SAKKWATO, FIRIMIYAN JIHAR AREWA NA FARKO KUMA NA ƘARSHE.
- Katsina City News
- 11 Oct, 2024
- 245
Yar Sarkin Bichi Abubakar ce, shi kuma Sarkin Bichi Abubakar ɗan Sarkin Bichi Mustapha ne. An haife ta a garin Bichi a shekarar 1923.
Ta fara karatun Addinin Musulunci tun tana da misalin shekaru 3 zuwa 4, ta kuma shiga Makarantar Elimentari ta Bichi a lokacin da takai kimanin shekaru 7, tana a Makarantar Midil sai aka aurar da ita ga mijinta, watau Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ɗan Sarkin Raɓah Ibrahimu, ɗan Sarkin Musulmi Abubakar II/Mai Raɓah, ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi.
Hajiya Amina Gwaggon Kano ce ta haifawa Sardaunan Sakkwato Sir Ahmadu Bello 'yayansa guda 3, watau Hajiya Fatima (Hajiya Inno ɗiyar Amadu) da Hajiya A'isha da kuma Hajiya Luba, duk da yake akwai ɗa namiji da ta haifa bayan haihuwar Hajiya Inno ɗiyar Amadu, kafin ta haifi Hajiya A'isha, ya rasu ne tun yana jinjiri.
Hajiya Fatima (Hajiya Inno ɗiyar Amadu) ta auri Mai girma Wamban Kano Alhaji Abubakar (Habu Ɗan Maje) ɗan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I, ɗan Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero, ɗan Sarkin Kano Malam Abbas, ɗan Sarkin Kano Malam Abdullahi Maje Karofi, ɗan Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo.
Hajiya A'isha ta auri Mai girma Marafan Sakkwato, Alhaji Ahmadu Ɗanbaba ɗan Magajin garin Sakkwato Usman wanda tsatso ne daga Magajin garin Sakkwato na farko, Malam Abubakar Ɗan Jada da aka fara naɗawa Magajin garin Cibiyar Daular Usmaniya a cikin shekarar 1817.
Hajiya Luba kuma ta auri Mai girma Marafan Sakkwato, Alhaji Umaru Aliyu Shinkafi ɗan Alhaji Aliyu Bisije, ɗan Dagacin Gasma Muhamman(A Ƙaramar Hukumar Mulkin Karasuwa ta Jihar Yobe).
Waɗannan 'yaya da Hajiya Amina Gwaggon Kano ta haifa sun haifa mata Jikoki da Tattab'a kunne da dama.
Misali, Hajiya Fatima (Hajiya Inno ɗiyar Amadu) ita ce ta haifi Hajiya Hadiza wadda ta auri Tsohon Gwamnan Tsohuwar Jihar Sakkwato (Jihohin Sokoto da Kebbi da Zamfara na yau), Alh. Shehu Mohammed Kangiwa Turakin Argungu /Turakin Kabi na farko.
Hajiya A'isha ce ta haifi Hajiya Asma'u Uwargidan Mai girma Sarkin Sudan na Wurno, Alhaji Shehu Malami da Magajin Garin Sakkwato, Alhaji Hassan Ahmad Ɗanbaba da sauran su.
Hajiya Luba kuma ta haifi Hafsatu da Ahmadu da ake yi wa kinaya da Sardauna.
Daga cikin waɗannan 'yaya nata, Hajiya Luba ce ke raye. Kenan Allah ya karɓi rayuwar Hajiya Fatima (Hajiya Inno ɗiyar Amadu) da kuma Hajiya A'isha.
A yayin da Dakta Mamman Shata Katsina ya yi wa biyu daga cikin waɗannan 'yaya uku da Gwaggon Kano ta haifa Waƙa, watau "Hajiya Inno ɗiyar Amadu" da "Luba 'yar Sarkin Sudan Bello", shi kuma Makaɗa Alh. Musa Ɗanƙwairo Maradun a Waƙar da ya yi wa Mahaifinsu, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato mai amshi 'Ya wuce reni ba a yi mai shi, Amadu jikan Garba sadauki' ya jero su ne ya na cewa "Mai girma ɗan mai girma, Uban Luba baban A'i da Inno....
Allah ya karɓi rayuwar Hajiya Amina Sir Ahmadu Bello (Gwaggon Kano) a garin Sakkwato ranar 27/06/2004.
Allah ya jaddada rahama zuwa ga Magabatanmu duka, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.
Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya.
08149388452,
08027484815.
birninbagaji4040@gmail.com
Laraba, 02/10/2024.