ZAZZABIN FARAR MASASSARA (BAYAMMA, CIWON SHAWARA)
- Katsina City News
- 17 Aug, 2024
- 884
Ita ma dai wannan cuta, wato farar masassara, wasu kwayoyin cuta ne ke haddasa ta. Kuma tana iya faruwa ga kowane irin mutum, watau yaro ko babba. Kwayar cutar na zama cikin jikin dan-Adam a kalla daga kimanin kwanaki uku zuwa shida (3-6) kafin ta kyankyashe. Amma ga wadansu mutane kuwa ta kan dauki har tsawon kwanaki goma (10).
Wannan zazzabin ne wanda ke kawo canjin kalar jiki, ba ma kamar ga fararen mutane. Za a ga jijiyoyin jikinsu sun yi tsanwa sannan kalar idanuwansu za ta zama koranya a madadin farare. Idan wadanda ke fama da wannan cuta suka yi fitsari za a gan shi ya yi kore.
4.1 ALAMOMIN FARAR MASASSARA
Cutar na farawa kai tsaye da:
1. Zazzabi
2. Matsanancin ciwon kai
3. Tashin zuciya
4. Amai
5. Kwayar idanuwa za su zama koraye
6. Ciwon ciki
7. Aman jini
8. Fitsarin jini
9. Kashin jini
10. Rashin yin wadataccen fitsari, saboda harbuwar da kwakwalwa ta yi
11. Rashin yin wadataccen numfashi, saboda harbuwar da zuciya ta yi.
12. A wasu lokuta kuwa idan ciwon ya tsananta, za a ga mutum bai san inda kansa yake ba, daga nan sai mutuwa ta biyo baya.
13. Shessheka
14. A kan samu matsala wurin numfashi a lokacin da mai ciwon ya kwanta.
Wadannan su ne alamomin cutar farar masassara. Da zarar mutum ya fara ganin su, ko kuma ya ga mai su, to, sai a hanzarta zuwa asibiti mafi kusa domin neman magani. Allah Ya sa mu dace amin. Ya kare dukkanin al'umma, amin.
4.2 YADDA AKE KAMUWA DA CUTAR FARAR MASASSARA
Ana iya daukar wannan cuta ta hanyoyi da dama kamar haka:
1. Idan ya kasance akwai wanda ke dauke da wannan kwayoyin cutar, sannan sauro ya cije shi, sai ya dauki jininshi ya sanya ma wani mutum wanda baida cutar.
2. Jakuna (donkeys) kan yi fama da irin wannan cutar, saboda haka idan sauro ya ciji jakin da ya kamu da irin wannan cutar kuma ya ciji mutumin da bai dauke da ita sai ya sanya masa. (jaki-sauro-mutum).
3. Ana iya kamuwa da cutar a yayin da aka karawa wani gurbataccen jini da ke dauke da kwayoyin cutar.
4.3 YADDA CUTAR TAKE KASANCE CIKIN JIKIN DAN-ADAM
Idan sauro ya ciji mutumin da ke fama da cutar farar masassara, ta nan ne zai tsotsi jininsa tare da wadannan kwayoyin cutar. To, su wadannan kwayoyin cuta za su ci gaba da yaduwa a cikin jikin sauron har zuwa tsawon kwanaki hudu (4). A wannan lokaci ne idan sauron ya ciji mutumin da bai dauke da wannan cutar sai ya sakar masa ita. Sannan su wadannan kwayoyin cutar za su zauna a cikin jinin mutumin, daga bisani su ci gaba da yaduwa. Idan suka yi kwanaki uku (3) cikin jini, sai su harbi wadansu mahimman sassan jikin mutumin, tare da kawo tangarda gare su. Wadannan sassa sun hada da hanta, da kwakwalwa, da saifa, da kuma huhu. (mutum-sauro-mutum)
4.4 ILLAR DA WANNAN CUTA KAN HAIFAR
Ita dai wannan cuta na haifar da illoli da dama inda daga ciki su ne kamar haka:
1. Kumburewar tantanin dake lullube da kwakwalwa
2. Matsanancin rashin wadatar jini a jiki.
3. Ciwon zuciya
4. Ciwon hanta
Har ila yau wannan matsanancin ciwo ne inda ya yi kama da ciwon nan na hanta (hepatitis). Kwayar cuta (virus) ke kawo shi kuma ana samun cutar ta hanyar cizon sauro kuma an fi samun cutar a karkara inda ke da jakuna.
A wasu lokutta cutar na zamowa annoba inda za a samu mutane da yawa suna fama da cutar a wuri daya. Wasu cutar ba ta tsananta masu, wasu kuma tana tsananta har ya zamanto zasu rinka yin habo, ko aman jini, ko suma sannan idan ba tarbo abin cikin sauri ba sai a rasa rai ko rayukkan mutane da dama.
6.0 TARUWAR RUWA A CIKIN HUHU
Wannan wani ruwa ne wanda ke taruwa a waje daya a cikin huhu na sashen hagu ko dama. A wasu lokutta kuwa duka huhun biyu na iya kamuwa. Hakan na faruwa ne dalilin wasu cututtuka wadanda marar lafiyar ya sha fama da su. Misali cutar pneumonia ko kuma tarin fuka.
6.1 ALAMOMIN CUTAR
Sune kamar haka:
1. Zazzabi tare da rashin sha'awar cin abinci.
2. Yawan yin tari wanda ya ke kasancewa tare da majina, kuma majinar idan an sunsuna ta za a ji tana wari. A wasu lokutta, kuma majinar na gauraye da jini
3. Ciwon kirji.
6.2 YADDA ZA A GANE SHIGAR CUTAR A JIKI
Ana iya gane shigar cutar ta wadannan hanyoyi kamar haka:
1. Ta hanyar daukar hoton kirji
2. Aunon majina
Wadannan aune-aune, duka asibiti ake yinsu. Saboda haka mutum da ya ga wadannan alamomi sai ya hanzarta zuwa asibiti mafi kusa domin neman magani. Da fatan Allah Ya sa mu dace, amin.
6.3 YADDA ZA A KULA DA MARAR LAFIYAR
Abu mafi a'ala a nan, shi ne a gane abin da ya haddasa taruwar wannan ruwa a huhu, sannan a yi maganinsa. Misali idan cutar pneumonia ce ta kawo shi, sai a ba mutum magungunan cutar pneumonia. Idan duk an yi maganin amma cutar bata warke ba to, a asibiti za a janye shi wannan ruwa da ya taru a huhun. Kuma a wasu lokutta ana yin aikin tiyata a asibiti domin a cire wani bangare na huhu. Da fatan Allah Ya kare mu; Amin.
6.4 YADDA ZA A GANE CUTAR
Ta hanyar duba marar lafiya, inda za a auna zuciyarsa, da gabba, da lakka, da fatar jiki, tare da daukar hoton kirjinsa. Sannan za a auna kashi ko majinar wanda ake zaton yana dauke da wannan cutar. Ta hanyar auna jininsa. Jini sun kasu kashi daban-daban. Daga ciki akwai nau'in jini wanda aikinshi ne ya kare jiki daga kamuwa daga wasu cututtuka, akwai kuma masu sa jini ya kasance cikin inganci. To, yayin da a cikin jinin marar lafiyar aka ga cewar kwayoyin masu kare jiki daga kamuwa daga wasu cututtuka za a ga sun yi sama (Adadin yawan su shi ne 6-11 000 a duka jinsi watau maza da mata). Idan ya daram ma hakan, to, yana nuna cewa akwai wannan kwayar cutar a cikin jini. Kuma masu sa ingancin jini za a ga sun yi kasa. (Su kuma adadinsu shi ne miliyan 5-5.5 a maza, amma ga mata shi ne miliyan 4-5.5). Shi kuwa wannan awo a asibiti ne kadai ake yin sa.
6.5 YADDA ZA A KULA DA MASU FAMA DA WANNAN CUTAR
1. Ana basu abinci marar gishiri
2. A samu hutu zuwa wani dan lokaci
3. Maganin da aka rubuta a kiyaye shan shi ka da ayi sakaci
YADDA ZA A KIYAYE DAGA KAMUWA DA CUTAR FARAR MASASSARA
1. Yin allurar rigakafi wadda ta kan yi aiki cikin jikin mutum har na tsawon shekaru goma
2. A kiyaye da tsabtace mahalli
3. Ta hanyar kebe wadanda suka riga suka kamu da cutar.
Da fatan za a kiyaye, amin summa amin.
Mun Ciro daga littafin Kula da Lafiya na Safiya Ya'u Yamel