TARIHIN KOFAR KAURA, KATSINA.
- Katsina City News
- 16 Jul, 2024
- 537
Kofar Kaura ta Samo sunantane daga Sarautar Kauran Katsina tun lokacin Sarakunan Habe. Sarautar Kaura babbar Sarautace domin tun lokacin Habe Kaura shine yake shugabantar babbar rundunar Yaki. Kauran da zaa iya tunawa a lokacin Habe shine Kauran Katsina Kuren Gumari. Kuren Gumari shine ya jagoranci Yaki Katsina da Gobir a shekarar 1795, lokacin da Katsina taci Gobir da Yaki a lokacin Sarkin Gobir Yakuba. A halin yanzu wasu daga cikin yan'uwan Kuren Gumari suna Tasawa wadda yanzu take a Jamhuriyar Nijar, wasu Kuma suna Tsafe ta Kasar Zamfara.
Haka Kuma a Lokacin Jihadin Shehu Usman, na karni na 19, a Katsina Ummarun Dallaje da sauran Mujahidai sun gudanar da Jihadi, inda aka Kori Habe suka gudu suka koma Maradi. Muhammadu Na banye Yana daya daga cikin wadanda suka taimakama Ummarun Dallaje ya gudanar da Jihadi, bayan cin nasarar Jihadi, an nada Na banye a matsayin Kauran Katsina, bayan rasuwar Na banye dansa Kaura Abubakar ya gajeshi. Har ya zuwa yanzu zuruar Na Banye ne suke rike da Sarautar Kauran Katsina Kuma gidansu na nan a Unguwar Kofar Kaura.
Kofar Kaura tana nan akan hanyar Katsina zuwa Kano a sashen Wakilin Kudu. Wannan Unguwa tana da mahimmanci ta fuskar tsaro, domin ta wannan sashen ne Kanawa suka rika kaima Katsina Hari zamanin Sarakunan Habe. Kofar tana Kuma da mahimmanci ta fuskar kasuwanci da zirga-zirga daga Katsina zuwa garuruwannan kudancinta.
Alhaji Musa Gambo Kofar soro.
16-07-2024.