KIWON LAFIYA: Hanyoyin Kariya daga Cutar Zazzabin Taifod da Yadda suke Yadawa
- Katsina City News
- 14 Jul, 2024
- 602
This title summarizes the main points of the article and indicates its focus on both prevention methods and the spread of typhoid fever.
Cutar Zazzabin Da Kan Kama ‘Yan Hanjin Mutum Watau Zazzabin Taifod
1.1
Shi dai wannan zazzabi wasu kwayoyin cuta ke haddasa shi. Watau idan suka shiga cikin jiki, sai su je wajen ‘yan hanji su kawo illa gare su. Wadannan kwayoyin cuta akwai wadanda ake iya gani da ido, ko kuma wanda marar lafiyar ya fada. To, amma kwayoyin cutar da ke sa zazzabin taifod, kwayar cutar bakteriya ce wadda ake iya magani.
Cutar ta kan kama ‘yan hanjin ɗan’Adam inda take sa wanda ya kamu da cutar ciwon da sauran alamomin da zan bayyana su daga baya.
1. Yin Allurar Riga-Kafi:
Wannan yana da amfani musamman ma idan an samu barkewar wata cuta kamar amai da gudawa. Haka kuma tana da amfani ga jarirai da zarar an haife su. A yi musu allurar riga kafin (BCG) tare da sinadarin vitamin A. Sannan duk bayan wata daya a maida shi asibiti domin karbar sauran alluran. Hausawa na cewa, "Riga kafi ya fi magani."
2. Tsabtace Muhalli:
Ta hanyar fadakar da mutane kan amfanin lafiya da yadda za su kula da lafiyar jikinsu tare da tsabtace wuri. Domin tsabta tana da mahimmanci kwarai da gaske kuma cikon addini ce. A tsabtace abincin da za a ci tare da ruwan sha, da mahalli.
3. Bayi:
Dole ne bayi su kasance kullum a rufe, sannan idan yaro ko mara lafiya ya yi amfani da kwano ko fo domin yin fitsari ko bayan gari, sai a zubar da shi cikin bayi kuma a wanke abin da aka yi amfani da shi sannan a mayar da shi inda aka dauko shi, kafin a sake amfani da shi.
4. Kiyaye Kayan Aiki:
Kiyaye kayan aiki ta hanyar tafasa su. Yadda ya kamata a kiyaye tare da yin amfani da sinadaran da ke hana yaduwar kwayoyin cuta kamar Dettol, bleach ko sevelon. Wasu lokutta kuma wadannan sinadaran kan kashe kwayoyin cuta.
5. Kebewa:
A kebe wadanda suka riga suka kamu da cutar a wuri na daban don hana wadanda ba su da cuta kamuwa.
6. Bincike da Gane Masu Cutar:
A bincika tare da gane wadanda ke dauke da cutar sannan a taimaka musu da magani. Wadanda suka riga sun kamu kuma an yi masu magani sun warke, su yawaita zuwa asibiti domin a duba lafiyarsu a kalla sau daya ko sau biyu a wata. Wannan yana da amfani kwarai da gaske domin sau da yawa idan cuta ta kama dan’Adam, ko an yi magani wasu sai su yi kamar sun warke, amma cutar ba ta fita daga jikinsu kwata-kwata ba. Misali cutar zazzabin taifod.
Har ila yau, wannan cuta tana yaduwa daga wurin mutanen da suke dauke da cutar zuwa ga wadanda suke tare da su. Misali, cutar zazzabin taifod wadda a yau ta yi ma mutanen Afirka katutu.
A takaice, wadannan su ne hanyoyin da kwayoyin cutar da ake dauka kan shiga cikin jikin dan’Adam tare da kawo masa illa. A wasu lokuta ma, cutar na haddasa rasa rayukan mutane maza da mata, yara da manya. Da fatan za mu kula da kyau, Allah kuma ya ba mu ikon kare jikin namu domin hana su kamuwa da irin wannan cututtuka. Amin.
Mun Ciro maku daga Littafin "Kula da LAFIYA na Safiya Ya'u Yemal