ASALIN BIKIN SALLAR GANI A MASARAUTAR DAURA.
- Katsina City News
- 13 Jul, 2024
- 538
Gani wani biki ne Wanda ake yi a Kasar Daura kowace shekara. Bikin Gani ya samo asalin shi daga kalmar Gani, watau " TARO" (Meeting). Bikin Sallar Gani a Daura ya Samo asalin shine daga Taron da Sarakunan Hausa suke yi duk shekara a Daura, domin a wancan Lokacin Daura itace tushen Kasar Hausa, shiyyasa ma ake Mata kirari da ta Audu tushen Hausa. A wajen wannan Taron ne Muhimman abubuwa da suka shafi tattalin arziki, da Siyasa da tsaro duk ana tattaunasu, sannan Kuma a samu matsayar da zaa magance su. Kowane Sarki zai Fadi matsalar dake tattare dashi a wajen wannan Taron, sannan Kuma Sarakunan Hausa sun kawo Jiziya wadda ake tattarawa a aikama Sarkin Borno( Mai Borno) a wancan Lokacin. Wannan Yana daya daga dalilin da yasa lokacin da Masu Jihadi suke yakar Sarakunan Hausa suka nemi Gudunmuwa wajen Sarkin Borno, Kuma ya taimaka masu akan masu Jihadi. Bayan an gama Taron ana Kuma shirya biki ga Sarakunan da suka halarci Taron, wannan shine asalin bikin Sallar Gani a Daura. Har ya zuwa yanzu zauren Gani yananan a Masarautar Daura inda Sarakunan Hausa suke Taruwa.
Hakanan Kuma a wajen wannan Taron ana nada Sarautu da dama ga bakin da suka halarci Taron daga kowane bangare na Kasar Hausa. Har ya zuwa yanzu Sarkin Daura ya rike wanna Al'adar ta Nadi, misali Sarkin Daura na yanzu Alhaji Umar Farouk Umar ya nada Marigayi Alhaji Ibrahim Ahmadu Kumasi a matsayin Garkuwan Kasar Hausa, ya Kuma nada Mai Shariar Ummaru Abdullahi Katsina a Matsayin Walin Hausa, ya kuma nada Alhaji Kabir Ya'u Yamel a matsayin Sarkin Aikin Kasar Hausa, da sauransu.
Amma Kuma daga baya lokacin da addinin Musulunci yayi karfi sosai a Kasar Hausa, bikin Sallar Gani ya canza salo, inda ya Kona ana gudanar dashi aduk lokacin Mauludin Nabyi Sallalahu Alaihi Wasallam, don taya murna ga zagayowar haihuwar fiyayyyen halitta Annabi Muhammadu Sallahu Alaihi Wasallam. A halin yanzu bikin Gani ana gudanar dashi duk ranar 12 ga watan Rabial.Awwal na kowace shekara.
Shima bikin kamar Shirin Hawan Sallah ne da Dawakai da Hakimmai da sauran Mayakan Sarki.