Hadin Gwiwar Tsaro: Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya ta Karbi Bakuncin Tawagar ‘Yan Sanda daga Dubai
- Katsina City News
- 03 Jul, 2024
- 561
Maryam Jamilu Gambo, Katsina Times
Abuja, Najeriya: Sufeto Janar na 'Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, a yau Laraba 3 ga watan Yuli, ya karbi tawagar manyan jami’an ‘yan sanda daga Dubai a Hedkwatar 'Yan Sanda da ke Abuja, matakin da ke da muhimmanci wajen karfafa hadin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
A yayin taron, IGP ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa wajen tabbatar da tsaron al'ummomin kasashen biyu, yana mai nuna cewa akwai dimbin 'yan Najeriya da ke zaune, aiki, da kasuwanci a Dubai, haka kuma akwai 'yan UAE da dama da ke zaune da kasuwanci a Najeriya, don haka karfafa hadin gwiwa zai tabbatar da kare muradun 'yan kasashen biyu.
A matsayinsa na Shugaban Kwamitin Shugabannin 'Yan Sanda na Yammacin Afirka (WAPCCO), IGP ya bayyana muhimmancin wannan ziyara wajen karfafa dangantakar 'yan sanda ba kawai tsakanin Najeriya da Dubai ba, har ma a fadin yankin Yammacin Afirka, yana mai sha'awar amfani da wannan dama don inganta hadin gwiwar tsaro, wanda zai amfani dukkan yankin.
Jagoran tawagar ‘yan sanda na Dubai, Birgediya Janar Adel Ahmad Moosa Sanqoor, Mataimakin Babban Darakta na Binciken Manyan Laifuka, ya bayyana godiyarsa bisa kyakkyawar tarba da suka samu kuma ya jaddada aniyarsu ta yin aiki tare da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya a fannoni da dama na jin dadin juna, ciki har da raba bayanan sirri, shirye-shiryen horo na hadin gwiwa, da ci gaban fasaha a harkar 'yan sanda.
An kammala taron da alkawarin kara zurfafa dangantakar tsaro da kuma binciko sabbin hanyoyin hadin gwiwa, wanda aka nufa don inganta tsaro da jin dadin al'ummomin kasashen biyu da yankin Yammacin Afirka baki daya.
Hoto: NPF