JAHADIN KATSINA, DA YADDA AKA KASA KASAR KATSINA GA SHUWAGABANNIN JIHADI.
- Katsina City News
- 14 May, 2024
- 415
Kasar Katsina kamin Jihadin 1804 tana karkashin mulkin Habe, zuruar Sarkin Katsina Muhammadu Korau. Acikin shekarar 1804 Mujaddadi Shehu Usman Danfodio yayi Kira da aka kaddamar da Jihadi, sannan Kuma a Jaddada addinin musulunci a Kasashen Hausa dama wasu makwabtanra kamar Nufe, da sauransu. A Katsina Mujahidai 3 sukayi takakkiya har Sokoto wajen Mujaddadi Shehu Usman Danfodio domin su amso tutar kaddamar da Jihadi. Bayan da suka Isa wajen Shehu Sai Shehu yaba Kowane daga cikinsu Tuta, wannan ya nuna Tutoci 3 Shehu ya bayar ga shuwagabanin Jihadi a Katsina sune 1. Malam Ummarun Dallaje. 2. Malam Na Alhaji da 3. Malam Ummarun Dunyawa. Bayan da suka dawo gida Katsina, anci gaba da gwabza Yaki da Sarakunan Habe, inda daga karshe su shuwaganin Jihadi sukayi nasara akan Sarakunan Habe, inda aka koresu suka gudu, suka bar Katsina, da farko sun fara zama Dankama daga nan Sai Damagaram, daga karshe suka dawo Maradi.
MIYA FARU KATSINA BAYAN CIN NASARAR YAKI DA KUMA KORAR HABE?
Kamar yadda bayani ya gabata cewa Mujahidai 3 aka ba Tuta, bayan cin NASARAR YAKI sai aka Kasa Kasar Katsina gida 3, kowane Mujahidun aka bashi bangarendshi.
1. Shi Malam Unnarun Dallaje shi ya zama Sarkin Katsina, Kuma shi ya shiga Gidan Korai, shi keda alhakin Kula da Masallacin Jumaaa na cikin birni, sannan Kuma ana gudanar da taro a Fadar shi. BAYAN haka akwai bangarorin da yake Kula dasu acikin Birnin Katsina.
2. Malam Na Alhaji ya rasu a cikin shekarar 1807 Sai aka dauko babban danshi Mai suna Muhamman Dikko, aka bashi Sarautar Magajin Malam, Wanda daga baya ta koma Yandakan Katsina, ya kafa Fadar shi a Zakka daga baya ta koma Tsauri, Wanda ya yanzu ta dawo Dutsinma. Sannan Kuma ya shiga Gidan Yandakan Katsina dake Unguwar Yantaba ta Kofar Yandaka a matsayin gidanshi na cikin Birnin Katsina. Gaban shiyyar Kurfi, da Tsauri da Ruma da sauransu Suma karkashin ikon shi.
3. Sai na 3. Malam.Ummarun Dunyawa shi aka Sarautar Sarkin Sullubawa, Wanda ya kafa Fadar shi a Zandam.da Bugaje. Sannan ya zauna Gidan Sarautar Sarkin Sullubawa dake Unguwar Sarkin Sullubawa dake Kofar Guga. Kasar Zandan, Bugaje, Kaita, Gazawa, Tasawa, Garabi da Sauransu duk suna karkashin ikon shi. Wannan hakin Katsina ta tsinci kanta a wancan lokacin. Wanda kowane daga cikin ShuwagabannnJihadi 3, Babu Mai shiga shiyyar kowa.
Ana cikin wannan halin wata Rana Shi shi Ummarun Dunyawa ( Sarkin Sullubawa ) ya tura Wakilin shi na Maradi, Mai suna Mani Asha, da yaje ya anso Mashi Haraji a Maradi, tunda Kasar Maradi a wancan lokacin tana karkashin ikon shi. To su Kuma Maradawa dama sun shiirya cewa zasu kashe Mani Asha, saboda sun gaji da mulkin shi. Haka Kuma sukayi suka kashe Mani Asha suka Kuma aikama Sarakunan Habe dake zaune Damagaram cewa sudawo Maradi suci gaba da mulki, saboda sun kashe Wakilin Katsina watau Mani Asha. Wannan shine dalilin zuwan Sarakunan Habe ( Jikokin Korau ) a Kasar Maradi. Kuma shine asalin Sarautar Sarkin Katsina Maradi, Wanda har yanzu sune suke mulkin Maradi.
HARIN MARADI A KATSINA.
Bayan da Habe sula kafa Sarautar Maradi, Sai Kuma suka kudiri aniyar kwatar mulkinsu daga hannun Fulani Dallazawa. Wannan harin ya faro ne daga Kasa Ummarun Dunyawa Sarkin Sullubawa, inda suka mamaye Gazawa, da Tasawa, da Garabi da Sauransu. Babban dalilin da yasa Yakin Katsina da Maradi ya dade shine rabuwar da Katsina tayi ga shuwagabanin Jihadi domin kowa ne daga cikinsu baida ikon shiga Kasar wani, wannan damar ce Habe suka samu, suka mamaye Kasar Sarkin Sullubawa da suka hada da Maradi, da Tasawa, Gazawa da Garabi da Sauransu. Wannan hare haren yasa shi Ummarun Dunyawa yayi hijira daga Zandam ya dawo Bugaje da zama, hakanan shima Malam Yusuf Na Garabi daya daga cikin mataimakan shi Ummarun Dunyawa yayi Hijira daga Garabi ya dawo Kafin Soli, bayan Kurfi ta fashe aka umarce shi ya dawo Kurfi yaci gaba da mullki. Amma abin lura shi Kasar Kurfi Kasar Yandaka ce a lokacin, to Amma shi Yusuf na Garabi ya zauna dashi da Takawanshi a matsayin suna amsar Umarnin su daga Sarkin Sullubawa, haka akai ta tafiya zuwa tsawon lolaci.
Gani wannan matsalar ta rabu, a dai dai wannan yanayin Sai Sarkin Musulmi Muhammadu Bello (1817-1837) ya ziyarci Katsina domin ya shawo kan al'amin ya inda ya Kara tabbatar da Ummarun Dallaje a matsayin Sarkin Katsina, ya Kuma umarci sauran Shwagannin Jihadi da suci gaba da amsar Umarnin daga gareshi, saboda gudin Yakin basasa a tsakanin su. Domin kamin wannan lokacin an fara samun rashin jituwa tsakanin shuwaganin Jihadin, saboda akwai lokacin da Yan Barga na Ummariun Dallaje suka Kai samame a Gidan Sarkin Sullubawa dake Kofar Guga, inda suka fataki mutanen Sarkin Sullubawa, Wanda daga nan ya tashi daga cikin birni ya koma Bugaje da zama baki daya, Sai daga baya ya dawo bayan sunyi Sulhu a tsakanin su, Dr. Yusuf Bala Usman ya ambaci haka a Littafin shi, The Transformation of Katsina.
Musa Gambo Kofar soro.