Jami'ar NOUN za ta ba Hafsatu Abdulwaheed da Innocent Chukwuma digirin girmamawa
- Katsina City News
- 09 Apr, 2024
- 574
Za ta yaye ɗalibai 22,175
BUƊAƊƊIYAR Jami'ar Nijeriya (NOUN) za ta bayar da digirin girmamawa na dakta ga wasu hamshaƙan 'yan Nijeriya biyu, wato Hajiya Hafsatu M.A. Abdulwaheed da Cif Innocent Chukwuma, a ranar Asabar mai zuwa.
Mataimakin Shugaban jami'ar, Farfesa Olufemi A. Peters, shi ne ya bayyana haka a wajen taron manema labarai da ya yi a Abuja a ranar Litinin kan bikin yaye ɗalibai karo na 13 da jami'ar za ta gudanar a ranar Asabar mai zuwa.
Daraktan Yaɗa Labarai na jami'ar, Malam Ibrahim Sheme, ya faɗa a cikin takarda ga manema labarai cewa ita dai Hajiya Hafsatu Abdulwaheed, ita ce mace ta farko a arewacin Nijeriya da ta wallafa littafin hikaya, sannan sananniyar 'yar gwagwarmaya ce mai rajin tallafa wa al'umma.
Littafin ta, So Aljannar Duniya, an wallafa shi ne a cikin 1974.
Shi kuma Cif Chukwuma, shahararren ɗan kasuwa ne wanda ya assasa Innoson Motors, wanda shi ne kamfanin harhaɗa motoci na farko na 'yan ƙasa da aka kafa a Nijeriya.
A taron manema labaran, Farfesa Peters ya ce za a ba Hajiya Hafsatu Abdulwaheed digirin girmamawa na Daktar Wallafa ne (wato Doctor of Letters, honoris causa).
Ya ce: "Ta sadaukar da rayuwar ta ga hidimar haɓaka harkar ilimi, musamman na 'ya'ya mata, bisa amanna da cewa iya karatu da rubutu yana da ƙarfin sauya matsayin al'umma tare da karya lagon fatara da yunwa."
Shi kuma Shugaban kamfanin Innoson Motors za a ba shi digirin ne a fannin Gudanarwar Kasuwanci (Business Administration) saboda ya ciri tuta a fagen "ƙirƙira, assasawa, tare da sadaukarwa ga amfani da kayan aiki na cikin gida."
Ya ƙara da cewa ayyukan waɗannan mutane biyu da za a karrama "sun yi daidai da ainihin burukan NOUN na asali na haɓaka ilimin kasuwanci, samar da ababen ilimi, da kuma ƙirƙira."
Jagoran jami'ar ya yi nuni da cewa NOUN ba ta cika bayar da digirin girmamawa ba, domin na ƙarshe da ta bayar tun cikin 1995 ne, saboda haka sai da ta yi zurfin tunani kafin ta yanke irin wannan shawarar.
Peters ya ce wannan girmamawar da za ta yi babbar nasara ce ga al'ummar jami'ar kuma hanya ce da za a samar da kyakkyawan haɗin gwiwa da ya ginu kan harkar ilimi.
Haka kuma jagoran ya bayyana cewa a bikin na bana jami'ar za ta yaye ɗalibai 22,175 waɗanda daga cikin su guda 15,768 masu digirin farko ne daga tsangayu takwas na jami'ar, sai 6,407 masu digiri na biyu, da ɗalibai shida masu digiri na uku.
Kafin ranar Asabar da za a yi bikin, za a ƙaddamar da sabon Shugaban Jami'a, wato Oba na Benin, Oba Ewuare II, a ranar Alhamis, kuma za a yi taron laccar yaye ɗalibai wadda Mataimakin Shugaban Buɗaɗɗiyar Jami'ar ƙasar Tanzaniya, Farfesa Elifas Bisanda, zai gabatar a ranar Juma'a.